Menu

Ko kun san yanayin kwanciyar da ta fi dacewa lokacin barci?

15186720 Hoton alama

Sun, 27 Aug 2023 Source: BBC

Akwai mutanen da suke da yawan gumi ta gefe guda a barcin dare, wasu kuma ta baya suke gumin. Amma wane yanayin bacci ne ya fi hutar da gajiya?

Idan kana rayuwa a yankunan da ke fama da tsananin zafi a wannan lokaci, babu mamaki ka shafe dare kana ta juyi, ka gwada salo daban-daban domin ganin bacci ya kwashe ka. Amma me bincike ke cewa dangane da yanayin kwanciyar bacci mafi dacewa?

Wani bincike da aka gudanar kan ma'aikatan jirgin ruwa da ke dakon kaya da masu aikin walda a Najeriya na iya taimaka mana, duk da cewa bacci abu ne mai muhimmanci a garemu, yanayi na tattare da ban mamaki ganin cewa babu wani nazari mai zurfi da aka yi kan wannan batu.

Na farko akwai bukatar fahimtar yanayin kwanciyar baccin mutane. Kana iya tambayarsu kai-tsaye, sai dai galibi muna tuna namu baccin ne a lokacin da muke kokarin bacci da kuma yanayin da muke tashi.

Domin samun karin haske, masu bincike sun gwada abubuwa daban-daban ciki harda naar mutane lokacin da suke bacci ko kuma a daura musu na'urar da zata ke naɗar abubuwan da suke yi.

A Hong Kong masu binciken sun bijiro da abin da ake kira ''Bargo tantace baccin mutane, da ke kunshe da wata kamara da ke iya ganin yada mutum ke bacci ko da yana cikin bargo mai kauri.

Masu bincike a Denmark sun yi amfani da wasu kananan nau'rori da ake makalawa a bayan mutane da kafaɗa kafin su kwanta domin gane yanayin baccin su.

Sun fahimci cewa a lokacin baccinsu a gado, mutane na shafe kusan rabin lokacin baccinsu a bangare guda, kusan kashi 38 cikin 100 a rigingine, yayin da kashi 7 cikin 100 ke ruf-da-ciki. Yanayin shekaru da manyanta, na sauya tsawon lokacin karuwa baccin su a gicciye.

Bambanci da ake samu kan bacci a gicciye yanayin ne da ke zuwan mana da girma, saboda da wuya ka samu yara musammn daga shekara uku su kwanta a gicciye na tsawon lokaci ko a rigingine ko ruf-da-ciki.

Jarirai, akasari, a rigingine suke kwanciya saboda haka ake kwantar da su saboda wasu dalilai na lafiyarsu.

Don haka bacci a gicciye shi yafi yawa kuma dole muyi ammana da abin da yafi rinjaye domin zaɓen yanayin bacci mafi dacewa da mu, amma kuma ina batun kididdiga?

Wani ɗan bincike kan yada mutane za su kwanta ya nuna cewa mutanen da ke kwanciya ta ɓangaren dama a gicciye sun fi daɗin bacci kan masu kwanciya ta ɓangare hagu, sannan masu kwanciya a rigingine suka biyo baya.

Idan kana samun sauki wajen kwanciya a ɓangare guda, babu mamaki hakan ya kasance sauki ga duk mutumin da ke kokari bacci nan kurkusa.

A wani lokaci, da na kai ziyara da zagaye a kan wani jirgin ruwa a kokarin haɗa wani shirin rediyo ma'aikatan jirgin sun nuna mun dakunan baccinsu, gadajensu su kasance a matse da juna ta yada motsawa ma zai yi wahala. Hakan na nufin suna bacci ne a rigingine, sun ce a kodayaushe ana rige-rigen bacci kafin ɗakin ya batse da masu munshari.

Wani gajeren bincike kan ma'aikatan jirgin ya nuna cewa galibinsu munshari na tasiri da hannasu bacci yada ya kamata, shiyasa suke bacci a rigingine.

Galibin lokuta munsharin da mutane ke yi na da alaka da matsalolin bacci, inda a wasu lokutan numfashi ke katsewa, sai kuma can ya dawo. An fi samun irin wannan matsala ga mutanen da ke bacci a rigingine.

A madadin haka, bacci a gicciye na taimaka wajen numfashi da kyau da shakar iska da hana harshe toshe maƙoshi, ta wannan hanya mutum na iya munshari kadan.

A wasu lokutan kuma, sauya salon bacci daga rigingine zuwa kwanciya a gicciye na taimakawa wajen sasaita matsalolin bacci da kyau.

Sannan bacci ta gefe ko a gicciye na da wasu alfannu na daban. Misali, bincike kan yanayin kwanciyar bacci masu walda a cikin kwantainonin jirgin ruwa a Najeriya, ya nuna cewa masu bacci a rigingine su fi fuskantar barazanar ciwon baya da wuya, idan aka kwatanta da basu bacci a gicciye.

Sannan masu bacci a gicciye, na samun saukin ciwon baya da kuma wuya.

Amma wannan baya na nufin bacci a gicciye ga kowa ya kasance magani ga duk ciwuka. Ya danganta da abin da ke damun mutum da kuma yanayin kwanciyar bacci lokaci zuwa lokaci.

Wani bincike da aka gudanar a Yammacin Australia a gidajen mutane na tsawon sa'o'i 12 a cikin dare ta hanyar amfani da na'urar da ke naɗar bacci ya gano cewa mutanen da ke tashi bacci da ciwon wuya suna kwashe lokaci ne suna kwanciya a yanayin da masu bincike suka kira ''kwanciyar bacci mai haddasa wasu cututtuka''.

Wannan batu na iya haddasa abubuwa da dama a zukatarku, amma abin da yake nufi shi ne ka kwanta a gicciye ka lankwasa jiki, misali, daura kafafuwa kan juna, da lankwasa baya. Akasin haka, mutanen da ke bacci a miƙe, amma a gicciye na samun saukin ciwon wuya.

Ina kuma batun ka gwada wani salon bacci na daban, sannan ka bibbiyesu ka ga ko hakan zai kawo wani sauyi a tattare da su musamman kan ciwon da suke fuskanta.

A wani bincike da aka gudanar kan mutane masu shekaru da suka shiga wani shiri motsa jiki a Portugal, an umarci mutanen da ke ciwon baya su kwanta a gicciye, sannan masu ciwon wuya su kwanta a rigingine. Mako hudu bayan wannan gwaji kashi 90 cikin 100 na mutanen sun ce ciwonsu ya ragu.

Wannan alkaluma sun kasance kamar masu ɗaɗɗaɗa rai, amma akwai abin taka tsan-tsan. Mutane 20 ne kaɗai suka shiga wannan nazari - adadin da babu yawa - don haka abu ne mai wahala a yanke hukuncin cewa wannan salo ko yanayi na bacci zai yiwa kowa aiki idan ana fama da ciwon baya da wuya. Kamar yada bincike masana ke nunawa akwai bukatar sake inganta bincike.

Idan kana fama da ƙwarnafi, zai yi kyau ka gwada bacci a gicciye ta hannun hagu a nan gaba

Saboda dalilai na rashin lafiya, babu dalilin ka tsaya tambaya kan kwanciya a rigingine ko a gicciye, abin da kake bukata shi ne nazarin kwanciyar bacci mafi dacewa.

A lokacin ƙwarnafi wanda ke tasowa daga ciki yana zuwa kirji da haifar da kuna mai raɗaɗi. A wasu lokutan likitoci na shawartar mutane su yi kokari su kwanta a matashi mai tudu wanda zai taimaka musu samun saukin irin wannan raɗaɗi.

Idan yanayin ya cigaba ba tare da wani sauki ba, to ya zama cutar ulcer mai haɗarin gaske. Abin da ya sa hakan ke faruwa bai fito fili ba, amma abu guda da ake bayyanawa shi ne bacci a ɓangare guda na tasiri wajen kawo sauki ko ta'azzarar cuta. Bacci a yanayi da ya dace na kuma iya taimakawa wajen kawo sauki.

Sai dai kowanne yanayi mutum ya tsinci kai, indai matsalar ta ƙwarnafi ce, to akwai bukatar yawaita bacci ta ɓangaren hannu hagu a gicciye nan gaba.

Zuwa yanzu dai batutuwan namu sun fi karfi ne kan bacci a rigingine ko a gicciye, wanda galibin mutanen suka fi yi. Amma kuma ina batun masu bacci ta ruf-da-ciki? ko da yake masu wannan hali masu da yawa.

Wani bincike ya nuna cewa ba abu ne mai kyau ba, a rinka irin wannan bacci idan kana da ciwon haɓa, wanda kusan ba abin mamaki ba ne.

Ina kuma batun tamoji? Gaske ne, kife fuska a kan matashin kwanciya na ta'azzara tamoji?

Binciken da aka wallafa a mujallar da ke nazarin kwaskwarimar halitta, tawagar likitocin fata da kwaskware halitta, sun ce fatar fuskar mutum ba ta son takura ta fi son a daina jagwalgwala ta.

Abin da ya kamata a nan shi ne mutum ya riƙa sa fuskarsa ta inda zai riƙa samun iska babu takura, kenan babu batun kifar da fuska a lokacin bacci.

Sannan idan kare fata ya kasance abu mai muhimmanci gareka kan bacci mai kyau ko kuma fama da matsalolin kurajen fuska ko ciwo, to bacci a gicciye ne mafi dacewa.

Me za mu iya yi domin karkare duk wadannan bayanai? Abu na farko, idan komai lafiya, to kwanciya a gicciye ne mafi dacewa, duk da dai wasu lokuta akwai bukatar kula saboda kauce wa ciwon baya da wuya - sannan inda kake kwanciya na iya kara ko rage ƙwarnafi. Munshari na karuwa idan ka kwanta a rigingine, amma da yake mutane sun bambanta akwai bukatar ka nazari yanayin baccin da ya fi dacewa da kai.

Sannan akwai bukatar gwada salon bacci daban-daban da kuma fahimtar duk yanayin baccin da bai karbe ka ba sai a sauya. Amma dai kada a nace wa sauya salon bacci a kullum, domin hakan na iya hana ka bacci da kyau idan kullum mutum ya kasance cikin nazari

Source: BBC