Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
A baya-bayan nan ne Jam'iyyun hamayya bakwai a Najeriya ciki har da babbar jam'iyyar hamayya ta PDP suka ɗauki matakin yin gamin-gambiza ƙarƙashin Ƙungiyar Jam'iyyun da suka damu kan abubuwan da ke faruwa wato Concerned Political Parties (CPP).
Sauran jam'iyyun da suke cikin wannan haɗaka sun haɗa da NNPP da ADC da APM da SDP da YPP da kuma ZLP.
Jam'iyyun hamayyar sun yi taron gamayyar ne karon farko a ranar Laraba inda aka yi wata ganawa tsakanin jagororin jam'iyyun bakwai a sakatariyar jam'iyyar SDP da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Sai dai gamin gambizar bai haɗa da Jam'iyyar Labour ba, wadda ɗan takararta ya zo na uku a babban zaɓen Najeriya na 2023.
LP ta bayyana cewa jam'iyyun da suka yi wannan taron ba su tuntuɓe ta ba.
Shugaban Jam'iyyar SDP, Shehu Musa Gabam, a jawabin da ya yi wa ƴan jarida bayan taron, ya ce matakin da suka ɗauka wani yunƙuri ne na rage ƙarfin ikon da jam'iyyar APC ke da shi a siyasar Najeriya.
Wannan yunƙuri na jam'iyyun adawa dai batu ne da al'ummar ƙasar da kuma ƴan siyasa ke ta tsokaci a kai.
Toh ko ya jam'iyya mai mulkin ta ji da wannan yunƙuri?
A cewar sa, duk abin da ba a yi shi da safe ba, ba zai yiwu a yi shi da la'asar ba." kamar yadda ya faɗa.
Sai dai ya ce jam'iyyun za su iya cimma nasara idan suka haɗe suka gina jam'iyya ɗaya mai aƙida, suka kuma tsaya a bayan wani ɗan takara guda ɗaya.
A cewarsa, za su iya nasara wajen ƙalubalantar APC tare da yin nasara idan suka kashe kwaɗayinsu na son takara tare da dagewa wajen yin kamfe lungu da saƙo na ƙasar.