A makon da ya gabata ne Kotun Ƙolin India ta ce gwamnonin ƙasar za su iya lalata dumukuraɗiyyar ƙasar idan har abubuwan da suke yi suka haifar da faɗuwar gwamnatin wata jiha.
Kotun na magana ne a kan gwamnan jihar Maharashtra da ke yammacin ƙasar, wanda ya nemi a kaɗa wata ƙuri'ar ƙauna mai ka-ce-na-ce a majalisar dokokin jihar tasa a shekarar da ta wuce, wanda hakan ya kai ga faɗuwar gwamnatin jihar a lokacin.
Jam'iyyar Shiv Sena waddaa ita ce ta gwamna Uddhav Thackeray, ta kasance mafi girma a haɗakar gwamnatin jihar ta Maharashtra.
To amma wasu da suka yi tawaye sun raba jam'iyyar suka yi sabuwar haɗaka da jam'iyyar Firaminista Narendra Modi wato Bharatiya Janata Party (BJP), wadda ke mulkin ƙasar ta Indiya.
Daga nan ne sai gwamnan jihar, Bhagat Singh Koshyari, ya nemi a kaɗa ƙuri'ar nuna ƙauna a kan gwmnatinsa to amma sai nan da nan Mista Thackeray ya sauƙa a watan Yuni kafin a yi ƙuria'r, ya yarda cewa magoya bayansa sun ragu ba su da yawa.
Da yake sauraren wasu ƙararraki da aka shigar a kan batun a makon da ya wuce, Babban Mai Shari'a na India Dhananjaya Chandrachud ya ce wannan ƙuria' da gwamnan ya a aka yi ba ta dace ba.
Alƙalin ya bayyana cewa gwamnan ba shi da ikon shiga wani hurumi da zai iya haifar da faɗuwar gwamnati.
''Wannan abu ne mai haɗarin gaske ga dumukuraɗiyyarmu," in ji shi.
Wannan ba shi kadai ba ne domin a jihohin Kerala da Telangana da ke kudancin ƙasar, gwamnatocinsu sun zargi gwamnonin da ƙin sanya hannu a kan wasu kudurorin doka da za su zama doka.
A kan haka ne gwamnatin jihar Telangana ta nufi Kotun Ƙoli da zargin gwamnanta Tamilisai Soundararajan da haddasa tarnaƙi na tarin mulki.
Wata jam'iyya ce ta yanki take gudanar da mulki a Telangana, yayin da jihar Kerala ke ƙarƙashin haɗakar jam'iyyu masu ra'ayin kawo sauyi.
Dukkanin gwamnonin jihohin biyu da kuma na jihar Maharashtra, jam'iyyar BJP mai mulkin Indiyar ce wadda abokiyar hamayyarsu ce ta naɗa su
Su dai gwamnonin Indiya waɗanda shugaban ƙasa ne ke naɗa su bisa shawarar firaminista su ne shugabannin gwamnatocin jihohi a bisa tanadin tsarin mulki.
Duk da cewa kusan aikinsu na je-ka-na-yi-ka ne, suna da haɗakar iko na majalisar dokoki da ɓangaren zartarwa da kuma iko na kashin-kansu.
Idan aka samu rikicin siyasa, misali idan zaɓen jiha ya kasance bai kammalu ba (inconclusive), suna da ikon yanke shawara kan jam'iyyar da za ta kafa gwamnati.
Haka kuma gwamnoni suna iya kin sanya hannu a kan dokar da majalisa ta amince da ita.
A taƙaice dai shi gwamna a Indiya ana sa ran ya kasance kamar alƙali ne a tsarin dumukuraɗiyyarsu.
Sai dai duk da wannan matsayi da suke da shi gwamnonin sun daɗe suna ɗaukar ɓangare, inda sukan kasance tamkar ƴan amshin shata na gwamnatin tarayya.
Wani masanin tarihi Mukul Kesavan, ya nuna cewa yanayin yadda ake naɗin gwamnonin da kuma rashin tabbacin tsawon wa'adinsu hakan ya mayar da su tamkar ƙirƙirar gwamnatin tarayya a yanayin da ake jumurɗar siyasa maimakon su kasance alƙalai wadanda ba su da ɓangare.
Gwamnatin tarayya a Indiya takan kori gwamnonin da abokan hamayyarta suka naɗa, wanda hakan ke ƙara siyasantar da matsayin.
Wani nazari da aka yi a kan wa'adin gwamnonin ya nuna cewa daga shekarar 1950 zuwa 2015 kashi ɗaya bisa huɗu ne kawai na yawan gwamnonin suka kammala cikakken wa’adinsu na shekara biyar.
Kuma kashi 37 cikin ɗari ba su ma kai tsawon shekara ɗaya ba a kan muƙamin.
Akasari ma jam'iyya mai mulki kan saɓa al'ada ta naɗa mutum a matsayin gwamna ba tare da ta tuntunɓi gwamnatin jihar da aka zaɓa ba.
Wannan kan haifar da ƴar tsama tsakanin gwamnatin tarayya da kuma ta jihohi.
Tsawon gomman shekaru da dama jama'a na kallon gwamnoni a matsayin masu tsoma baki ko katsa-landan wajen tafiyar da harkokin gwamnatocin jihohin da aka zaɓa, waɗanda suke da saɓani da jam'iyya mai mulki a gwamnatin tarayya.
BK Nehru, wanda ya mulki kusan jihohin Indiya goma sha a tsawon aikinsa da ya ƙare a shekarun 1980, shi kansa ya taɓa bayyana muƙamin a matsayin na tsohon wani jigo a jam'iyya mai mulki wanda ya zama kusan maras sauran amfani, inda ake tura mutum can ya huta.
Ba mamaki wannan ne ma ƙila ya sa sai ƴan jam'iyya masu biyayya sosai ake naɗawa galibi a wannan matsayi domin saka musu kan biyayyar da kuma aikin da suka yi.
Wani nazari da Farfesa Ashok Pankaj ya yi a kan gwamnonin na Indiya daga 1950 zuwa 2015 ya gano cewa yawanci ƴan siyasa ne ko kuma tsofaffin ma'aikata da suka yi ritaya ake naɗawa a wannan muƙami.
Sauran kusan sun ƙunshi alƙalai da lauyoyi da jami'an tsaro da malaman jami'a.
Kashi ɗaya bisa biyar na dukkanin gwamnoni tsofaffin ƴan majalisa ne.
Wannan ne ya sa mutane da dama ke ganin lokaci ya yi da za a soke wannan muƙami na gwamnan jiha.
''Wannan ofishi ne da za a iya cewa bai dace ba sam-sam,'' in ji editan jaridar ThePrint, Shekhar Gupta.
Ya ce ba abin da zai faru idan aka wayi gari wata rana ba wannan ofis.
Sai dai ba faɗar ba aiwatarwar ita ce wahalar. Mista Kesavan na ganin cewa idan har ba za a iya yin dokar da za ta kawar da wannban muƙami ba, abin da yake ganin zai fi dacewa to shi ne a rage matsayin ta yadda za su samu shiga daidai yadda zai fi dacewa da su.
Wani cikakken nazari da wasu masana na ƙasar suka yi kan wannan muƙami na gwamna ( Heads Held High: Salvaging State Governors for 21st Century India), ya bayar da shawarar sake fasali da tsarin muƙamin maimakon soke shi.
Masanan sun bayar da shawara cewa bai kamata a ce jam'iyya mai mulki ita ke da ikon naɗawa da cire gwamna ba.
Suka ce kamata ya yi hakan ya kasance ana yinsa ta tsari na tarayya da haɗin kai yadda ya kamata.
Kuma ya kasance duk wani hukunci ko abu da gwamnan ya yi ya rubuta dalilinsa na yin hakan wanda za a bayyana ga jama'a.
Masanan suka ƙara da cewa ya kamata ya kasance ana naɗin a bayyane sannan su kada su kasance karnukan farauta ko ƴan amshin shata.