Menu

Kocin PSG, Galtier ya tabbatar Messi zai bar kungiyar

Lionel Messi

Sat, 3 Jun 2023 Source: BBC

Lionel Messi zai buga wa Paris St-Germain wasa na karshe a kungiyar ranar Asabar, inda da za ta fafata da Clermont in ji koci Christophe Galtier.

BBC ta yi rahoto a watan Mayu cewar mai shekara 35 kyaftin din Argentina zai bar kungiyar ta Faransa a karshen kakar bana.

Messi, wanda ya koma PSG a Yulin 2021, bayan da kwantiraginsa ya kare da Barcelona, ya bayar da gudunmuwar da kungiyar ta Faransa ta lashe Ligue 1 biyu.

''Na samu damar horar da daya daga fitattun ƴan wasan tamaula a duniya,'' in ji Galtier.

"Wannan shi ne wasan karshe da zai buga a PSG a Parc des Princes, ina fatan magoya baya za su yi masa tafin girmamawa da ya dace.

PSG ta kara daukar matakan tsaro a gidan Messi da Neymar da Marco Verratti da kuma Galtier a watan jiya, sakamakon zanga-zanga daga magoya bayanta.

Daga nan ne Lorient ta ci PSG, sannan aka dakatar da Messi mako biyu, bayan da ya je Saudi Arabia ba tare da izini ba - daga baya ya nemi afuwa.

Messi kyaftin din Argentina ya ja ragamar kasar ta lashe kofin duniya a 2022, bayan da ya koma Faransa da taka leda.

Tun farko sun cimma yarjejeniya cewar PSG za ta tsawaita masa kwantiragin da kaka daya, amma daga baya sai ya sauya shawara.

Messi ya ci wa PSG kwallo 21 ya bayar da 20 aka zura a raga a dukkan fafatawa a kakar nan, jimilla ya ci wa kungiyar kwallo 32 a karawa 74.

An fitar da PSG a zagayen kungiyoyin 16 a gasar Zakarun Turai ta Champions League a bana karo na biyu a jere.

Source: BBC