Menu

Komala: Matasan Iran na zama sojojin ƙungiyar bayan sun tsere daga ƙasar

 117311949 Femalekomalarecruitstraininthemountainsofiraqikurdistan Kurdistan na Iraƙi

Fri, 5 Mar 2021 Source: BBC

A kowace shekara fiye da Kurdawa 100 ne 'yan Iran, wasu daga cikinsu 'yan shekara 15, kan yi kasadar tsallaka iyakar ƙasar zuwa yankin Kurdistan na Iraƙi domin su shiga rundunar Komala.

Komala wata jam'iyyar siyasa ce ta Kurdawa waɗnda aka kora daga Iran kuma sansanin horarwar nasu bai wuce kilomita 100 ba daga Iran zuwa Kurdistan.

Domin su kai ga sansanin, sai sun tabbata sun kauce wa ababen fashewa da jami'an tsaro da sojojin harbi. Idan suka yi rashin sa'a, sojojin Iran kan kama su, inda za a tsare su, a tuhume su har ma yanke musu hukuncin kisa.

Dakarun Komala da ke aiki a ɓoye kan taiomake su a kan hanyar. Babban burin matasan Kurdawa - maza da mata - shi ne su sdamu shiga ƙungiyar Komala na peshmerga.

A sansanin, ana yi musu wani gwaji domin tabbatar da cewa babu 'yan leƙen asirin Iran a cikinsu sannan kuma ko za su iya jure wahalhalun da aikin ya ƙunsa.

Komala ta bai wa BBC damar shiga sansanin domin gane wa idonta yadda aka horar da matasa domin mayar da su 'yan gwagwarmyar siyasa da kuma mayaƙan peshmerga a tsawon shekara guda.

Wannan labari ya mayar da hankali ne kan mutum huɗu sabbin shiga ƙungiyar, maza biyu mata biyu, inda muka ga irin halin da suka shiga na ƙunci da wahala bayan sun bar gidaje da iyalansu tsawon mila-milai.

Bayan kafa ta a matsayin mai tsattsauran ra'ayin kawo sauyi a Iran a shekarun 1970, Komala ta shiga fafutikar sauke jagoran Iran Shah, amma daga baya sai Ayatollah Khomeini ya haramta ta.

Ya bayar da fatawa a kan jam'iyyar yana mai cewa mambobinta fasiƙi ne waɗnda ba sa son ci gaban addinin Musulunci da kuma juyin juya halin da ake ƙoƙarin yi.

Yanzu ƙungiyar na fafutikar nema wa Kurdawan Iran 'yanci waɗanda suke da yawa a arewa maso yammacin ƙasar. Ta ce ta bar wasu aƙidunta na kawo sauyi kuma rungumi tsarin dimokuraɗiyya wanda ba ruwansa da addini kuma zai kare 'yancin kowane ɗn ƙasa.

Sai dai har yanzu mambobin Komala na saka kakin sojoji kuma su ɗuki bindiga. Shugabanninta sun ce atasayen da ake yi da kuma ɗukar makamin na kare kai ne kawai.

Baya ga ayyukan da take yi a cikin Iraƙi, Komala kan tura dakarunta zuwa kan iyakar Iran domin ta nuna cewa har yanzu tana aiki da kuma nema mata mabiya.

Hukumomin Iran na kallon Komala a matsayin ƙungiyar 'yan ta'adda kuma takan kai wa sansanoninta hari a Iraƙi.

A labarin, dakarun Komala sun bayyana harkokin nasu da cewa gwagwarmyar siyasa ce domin yaƙi da zaluncin da ake yi wa Kurdawa.

Ba a karantar da harshen Kurdawa a makarantu, abin da ya sa matasa ke ganin cewa ana zaluntarsu ne ta hanyar hana su aikin yi da kuma shiga jami'o'in Iran.

Sun ce 'yan guraben da ake bai wa mata a Iran ya saɓa da aƙidar Kurdawa ta bai wa mata cikakken 'yanci. Maganar kisan kare kima wato honour killing da Ingilishi, ba halin Kurdawa ba ne.

Waɗannan dalilai da kuma burin kawo gyara game da rashin adalci ne ke sa matasan Komala shiga fafutikar.

Kasancewa ɗaya daga cikin mayaƙn peshmerga ba abu ne mai sauƙi ba, mayaƙan kan shiga cikin tsananin horon soja.

Da yawa daga cikinsu ba su taɓa yin nesa da danginsu ba, amma yanzu an hana su magana da su a wata uku na farkon shiga sansanin.

Ba dukansu ne ke gamawa ba. Wasu kan gudu zuwa Turai, wasu kuma su koma Iran. Sai dai waɗnda suka tsaya kan ci gaba da zama a matsayin dakarun peshmerga domin gudanar da abin da suka yi imanin cewa shi ne burin Komala.

Gwamnatin Iran ba ta ce komai ba game da wannan rahoto duk da cewa BBC ta tuntuɓe ta.

Source: BBC