Wata kotu ta bayar da Belin dan wasan Manchester United, Mason Greenwood, wanda ake zargin aikata fyade. Ana kuma tuhamar dan wasan mai shekara 21 da ikirarin zai yi kisa da nuna munanan halayen da ba su dace ba. An tsare dan kwallon a watan Janairu, bayan wasu hotuna da bidiyon da suka bayyana a Intanet, kan abubuwan da ake tuhumarsa. An ci gaba da tasre dan wasan a kotun Majistare ta Manchester da Salford tun daga ranar Litinin. Wani mai magana da yawun kotun ya tabbatar da cewar an bayar da belin Greenwood, amma bisa kan wasu ka'idoji. Ciki har da cewar ba za a tuntubi matar da ta shigar da kara ba, sannan ba zai zauna kusa da adireshin da yake Bowdon ba. Mista Greenwood bai halarci zaman kotun ba. Tun cikin watan Janairu aka bayar da dan kwallon beli, anma an sake tsare shi ranar Asabar, bayan da ya karya dokar da aka gindaya masa ta belin..