Menu

Kotu ta yankewa Hushpuppi hukuncin daurin shekara 11 a gidan kaso

29636696 Hushpuppi

Tue, 8 Nov 2022 Source: BBC

Wata kotu a Amurka ta daure dan Najeriyar nan da ya shahara a shafin sada zmunta da muhawara na Instagram, Hushpuppi sama da shekara 11 a gidan yari a kan samunsa da laifi a harkokin zamba a kasashen duniya.

 

Hushpuppi, wanda ainahin sunansa Ramon Abbas, ya yi fice wajen nuna rayuwar da yake yi ta facaka a shafinsa mai mabiya  miliyan 2 da dubu 800, kafin a rufe shafin a kwanakin nan. 

Alkalin kotun a Los Angeles ya kuma umarce shi da ya biya dala $1,732,841 ta diyya ga wasu mutum biyu da ya damfara.

A bara ya amsa laifin halatta kudin haram.

Haka kuma ya amince cewa ya so ya damfari wani mutum sama da dala miliyan daya, mutumin da  ya samar da kudin kafa wata makarantar yara a Qatar.

Dan damfarar ya yaudari mutumin ne inda ya say a bayar da kudi domin kafa makarantar, inda ya yi kamar shi wani babban jami’in banki ne, tare da kirkirar shafukan intanet na karya.

Kamar yadda wata sanarwa daga mukaddashiyar babbar lauyar gwamnatin Amurka  Tracy Wilkinson ta nuna a shafin intanet na ma’aikatar shari’ar Amurka.

Haka kuma Hushpuppi, ya amince da wasu tarin laifukan zamba da suka janyo asarar sama da dala miliyan 24.

Akwai kuma wasu da ake zargi da laifukan na zamba da suka shafe shi inda shi yake zama jigo a cikin ayyukan.

Abbas ya amince da aikata laifuka na zama da dama ta intanet da sauran hanyoyi da suka janyo asarar sama da dala miliyan 24, in ji ma’aikatar shari’ar ta Amurka.

Ramon Abbas, wanda ke harar Amurkawa da sauran mutane daga wasu kasashen duniya ya kasance daya daga cikin manyan ‘yan damafara a duniya, in ji Don Always mataimakin darekta a ofishin hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI, da ke Los Angeles.

Abbas ya rubuta wata wasika da hannunsa ga alkalin kotun Judge Otis D Wright inda yan una nadama kan laifukan da ya yi tare da cewa zai yi amfani da kudinsa na kansa ya biya wadanda ya damfara.

Sannan kuma y ace dala 300,000 kadai ya samu daga laifukan da aka yi masa sharia’a a kai.

Source: BBC