Menu

Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar Abba a matsayin gwamnan Kano

51626484 Abba Kabir Yusuf

Fri, 12 Jan 2024 Source: BBC

Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu a zaɓen gwamnan jihar Kano na shekara ta 2023.

Mai shari'a John Okoro wanda ya karanta hukuncin ya ce kotun ɗaukaka ƙara ta yi kuskure wajen tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar, wadda ta ce Abba Kabir bai samu rinjayen ƙuri'u a zaɓen ba.

Saboda haka nan kotun ta yi kuskure wajen zabtare wa Abba da NNPP ƙuri'u.

A game da batun rashin kasancewar Abba Kabir ɗan jam'iyyar NNPP, kotun ta ce jam'iyya ce kawai take da ikon tantance wanda ɗanta ne ko kuma a'a.

Saboda haka ne kotun ta amince da ɗaukaka ƙarar jam'iyyar NNPP tare da yin watsi da hukunce-hukuncen kotun ɗaukaka ƙara da kuma ta sauraron ƙorafin zaɓen jihar.

Wannan shi ne mataki na ƙarshe a turka-turkar da aka kwashe watanni ana yi game da sahihancin sakamakon zaɓen na gwamnan jihar Kano.

Tun da farko, kotun zaɓen gwamnan Kano a watan Satumban 2023 ce ta soke ƙuri'a 165,633 wadda in ji ta, aka yi wa ɗan takarar na jam'iyyar NNPP aringizo, bayan hukumar zaɓe a watan Maris, ta ce ya samu ƙuri'a 1,019, 602.

Gwamna Abba dai bai gamsu da hukuncin ba, don haka ya wuce zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Sai dai, ita ma kotun ɗaukaka ƙarar ta bai wa jam'iyyar APC nasara bisa hujjar cewa Abba ba ɗan jam'iyyar NNPP ba ne lokacin da aka tsayar da shi takara, don haka ta nemi a rantsar da ɗan takararta Nasiru Gawuna.

A ranar 20 ga watan Maris na 2023 ne Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan na jihar Kano.

Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen gwamnan, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri'u 890,705.

Source: BBC