BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Kotun zaɓen Najeriya za ta fara sauraron masu ƙalubalantar nasarar Tinubu

Hagu zuwa dama: Peter Obi, Bola Tinubu da Atiku Abubakar

Mon, 8 May 2023 Source: BBC

Mako uku daidai kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a Najeriya, kotu ta musamman za ta fara zaman sauraron ƙararrakin masu neman a rushe nasarar Bola Ahmed Tinubu a Litinin ɗin nan.

Zaman zai kasance a gaban alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara, waɗanda su ne suka ƙunshi masu shari'a a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta 2023.

Manyan 'yan adawan ƙasar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar Labour, kowannensu yana iƙirarin shi ne ya kamata INEC ta ayyana a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen 25 ga watan Fabrairun 2023.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta sanar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaɓen bisa hujjar cewa jam'iyyarsa ta APC ce ta samu ƙuri'u mafi rinjaye da aka kaɗa.

Ya dai samu adadin ƙuri'a 8,794,726, inda ya kayar da 'yan takara 17, cikinsu har da babban abokin fafatawarsa daga jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar wanda ya samu ƙuri'a 6,984,520 da kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour da ƙuri'a 6,101,533.

Sai dai wasu jam'iyyun adawa a ƙasar musamman PDP babbar mai hamayya da ɗan takararta Atiku Abubakar da kuma Peter Obi da jam'iyyarsa ta Labour Party sun ce suna ja kan sakamakon.

Wasu rahotanni sun ce a ranar farko ta zaman sauraron ƙararrakin, shugabar Kotun Daukaka Ƙara, Mai Shari'a Bolna'an Monica Dongban-Mensem za ta ƙaddamar da kotun tare da alƙalan da za su jagoranci zaman a hukumance.

Matakin da zai ba da damar zaman tattauna batutuwan share fage da kuma cimma matsaya kan buƙatun da aka gabatar, sannan a fitar da jadawalin zaman kotun gadan-gadan.

Haka zalika, ana sa rai lauyoyin 'yan takara za su yi musayar yawu kafin cimma matsaya a kan shaidu da bayanan da za a gabatar gaban alƙalan kotun a matsayin shaida.

Atiku da Peter Obi kowannensu ya shigar da ƙararsa daban, yana son kotun ta rusa nasarar Bola Tinubu, bisa iƙirarin cewa sakamakon zaɓensa na cike da kura-kurai da sauran matsaloli, sannan ta ayyana shi a matsayin halattaccen wanda ya yi nasara.

Sai dai, ɓangaren zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Tinubu, yana da'awar cewa an yi zaɓen gaskiya da adalci don haka yana neman a kori ƙorafe-ƙorafen.

Ƙarin masu ƙorafi a kan nasarar ɗan takarar APC a zaɓen watan Fabrairu har da ɗan takarar Action Alliance, Mr. Solomon Okangbuan da jam'iyyarsa AA da kuma ‘yar takarar jam’iyyar APM, Princess Chichi Ojei da jam'iyyarta, sai jam’iyyar APP.

Masu ƙalubalantar zaɓen Tinubu dai suna kafa hujjojin da gagarumin rashin aiki da kundin dokokin zaɓe na 2022 da kuma tsare-tsaren zaɓe da hukumar INEC ta gindaya a zaɓen watan Fabrairu.

Masu ƙorafe-ƙorafen sun kuma yi zargin cewa an tafka maguɗi da kura-kurai a zaɓen, saboda gazawar INEC na tura sakamako nan take ta hanyar laturoni daga rumfunan zaɓe zuwa Shafin Ganin Sakamakon Zaɓen hukumar wanda ake kira INEC Results Viewing Portal (IREV).

Jam’iyyar Labour da ɗan takararta a cewar rahotanni sun kuma yi iƙirarin cewa a lokacin zaɓen shugaban ƙasar, Tinubu da Kashim Shettima ba su cancanci tsayawa takarar ba.

Waɗanda ake ƙarar dai sun haɗar da hukumar zaɓe ta INEC da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Kashim Shettima da kuma jam’iyya mai mulki wato APC.

A baya ma, an sha ƙalubalantar zaɓen shugaban ƙasa a gaban kotun Najeriya.

Har yanzu a hukumance ba a sanar da alƙalan da za su jagoranci zaman kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen shugaban ƙasar ba.

Sai dai, tashar rediyon ƙasar mai suna Radio Nigeria ta ambato wata majiya a kotun ɗaukaka ƙarar na cewa rukunin alƙalan da tuni suka fara zama kan buƙatun wucin gadi da masu ƙorafin suka shigar, mai yiwuwa su ne za su ci gaba da shari'o'i bayan an ƙaddamar da kotun.

Rukunin alƙalan sun haɗar da Mai shari'a Haruna Tsammani da Mai shari'a Stephen Adah da Mai shari'a Abba Mohammed da Mai shari'a Joseph Ikyegh da kuma Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙarar Mai shari'a Monica Dongban-Mensem.

Kotun dai tana da tsawon kwana 180 wato kimanin wata shida don sauraro da yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen da aka shigar gabanta.

Daga bisani kuma, masu ƙorafi ko waɗanda aka yi ƙara za su ƙara samu tsawon wata biyu kimanin kwana sittin a matsayin lokacin sauraron ƙararrakin da za a ɗaga ga duk ɓangaren da bai gamsu da hukuncin kotun farko ba.

Source: BBC