BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Kovacic zai koma Man City kan fam miliyan 30

Mateo Kovacic

Wed, 21 Jun 2023 Source: BBC

Mateo Kovacic na daf da komawa Manchester City, bayan da Chelsea ta amince za ta sayar da shi kan fam miliyan 30.

Dan kasar Croatia, mai shekara 30 zai koma Etihad da taka leda kan fam miliyan 25 da karin fam miliyan biyar ta tsarabe-tsarabe.

Kovacic ya koma Chelsea daga Real Madrid a 2019, tun farko kan wasannin aro daga baya ta saye shi kan yarjejeniyar kaka biyar.

Zuwan Kovacic Etihad zai sa shakku kan makomar Ilkay Gundogan a Manchester City, bayan da yarjejeniyar dan kwallon Jamus ke daf da karewa.

Kovacic ya yi wa Chelsea wasa 37 a dukkan fafatawa a kakar da aka kammala, wadda kungiyar ta fuskanci kalubale, inda ta yi ta 12 a teburin Premier League.

Yana cikin 'yan wasan da suka lashe Champions League a Chelsea a 2021, bayan da Chelsea ta doke Manchester City 1-0.

Kovacic ya buga wa Croatia wasa 95 har da dukkan fafatawa a gasar kofin duniya a Qatar, inda kasar ta yi ta uku.

Source: BBC