Menu

Kun san illolin yawan teɓa na dogon lokaci?

Ansaf Azhar, Daraktan kula da lafiyar na gundumar Oxfordshire

Mon, 26 Jun 2023 Source: BBC

Wani daraktan kula da lafiyar al'umma ya ce tasirin yawan teɓa na dogon lokaci na iya zarta na annobar korona.

Ansaf Azhar ya ce ƙaruwar matsalar na ta'azzara sakamakon raguwar motsa jiki sanadin annobar.

Daraktan kula da lafiyar na gundumar Oxfordshire ya ce waɗanda lamarin ya fi shafa sun fito ne daga yankuna masu rauni.

Mista Azhar ya ce yana ƙoƙarin ganin motsa jiki ya sauƙaƙa musamman ga yara da kuma samar da ilimi game da abinci mai gina jiki.

Kimanin kashi 58 cikin 100 na manyan da ke Oxfordshire ne ke da ƙibar da ta wuce ƙima ko teɓa, kamar yadda ƙididdigar baya-bayan nan daga hukuma ta nuna.

Tsaka-tsaki a Ingila shi ne kashi 64 cikin 100.

Mista Azhar ya ƙara da cewa: "Wannan yana da yiwuwar haifar da babban illa ga lafiya fiye da annobar korona ita kanta," amma ya ƙara da cewa hakan zai faru na tsawon lokaci.

"Idan al'umma na fama da cuta, hakan ba abu ne mai kyau ba ga jama'a, hakan ba shi da alfanu wajen gudanar da aiki, ba shi da amfani ga tattalin arziki."

Daraktan kula da lafiyar ya ce tsarin rayuwar al'umma ya sauya sosai yayin da suka fito daga ƙangin annobar korona, sun zama ba sa yawan motsa jiki."

Ya ƙara da cewa kashi ɗaya bisa uku na yara ƴan aji shida na piramare suma sun kasance masu ƙiba fiye da ƙima.

Hukumar a baya ta ƙaddamar da wani shiri kyauta na tsawon mako 12 domin taimaka wa yara da iyalai sanin hanyoyin da za su lura da ƙiba.

Sue Pearce, wadda ke halartar shirin na Gloji Energy a Didcot tare da jkarta Lily Mae ta ce: "Yana matuƙar wahala a yanayin yawan aiki ka sami lokacin gano hakan da kanka.

"Ba wai yana magana bane kan nauyi ko gwada nauyi."

Mista Azhar ya ce ana buƙatar bin tsarin haɗaka da ta ƙunshi hukumomi da ma'aikata domin inganta lafiya da samar da abinci mai sauƙi da hanyoyin sufuri masu aiki da wuraren shuke-shuke.

Source: BBC