BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Kun san jirgin ruwan yawon shaƙatawa mafi girma a duniya?

Icon of the Seas | Royal Carribean

Thu, 13 Jul 2023 Source: BBC

A lokacin da zai fara aiki, zai zamo jirgin ruwa na shaƙatawa mafi girma a duniya.

Makeken jirgin na da tsawon mita 365, wato kimanin dogayen motocin bas guda 35 idan suka jera, kuma yana da nauyin tan 250,800.

Benen da ke cikin jirgin na da hawa 20, kuma zai iya ɗaukar mutum 10,000 – ciki har da fasinjoji 7,600.

Baya ga haka nan jirgin na da wasu abubuwa masu ban mamaki da ƙayatarwa.

Akwai wani makeken wurin wasan ruwa, wanda shi ne ya fi na kowane jirgin ruwa girma.

Akwai kududdufin ninƙaya guda bakwai.

Yana da makeken lambu mai cike da itatuwa.

A watan Janairun 2024 ne katafaren jirgin zai fara tafiya a tekun Caribbean.

Source: BBC