BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

'Kuraye na cin gawarwakin waɗanda suka mutu a yaƙi'

Tigray Armoured Car Hoto daga yankin Habasha | Hoton alama

Thu, 20 Oct 2022 Source: BBC

Kuraye suna cika cikkunansu da naman gawarwakin mutanen ƙauye, ana yi wa garuruwa da birane ruwan wuta ta sama, an tursasa wa tsofaffi da ƴan mata shiga aikin soja - duk waɗannan na daga cikin munanan labaran da ke fitowa daga yaƙin basasar Habasha, wanda ya yi sanadiyyar rayukan dubban ɗaruruwan mutane a yankin ƙasar na Tigray mai ɗinbin tarihi. A baya yankin ya kasance mai jan ra'ayin masu yawon buɗe ido, inda masu zuwa yankin kan ziyarci mujami'u da aka sassaƙa a cikin dutse, da wuraren tarihi na musulunci da kuma tsoffin litattafan da aka rubuta da harshen Ge'ez. Yanzu Tigray ya zama fagen daga, inda gamayyar dakarun Ethiopia da na Eritrea suke gwabza faɗa da na ƙungiyar masu rajin ƴanta al'ummar Tigray (TPLF), ana faɗa domin ƙwace iko da yankin wanda a baya ake wa kallon muhimmin ginshiƙi a siyasar Habasha - wanda a tarihi yake cikin yankin da ake kira Abyssinia. An kwashe watanni 17 yankin na a kulle - babu bankuna, babu sadarwar waya, babu intanet, sannan kuma ba a iya samun kafafen yaɗa labarai. A cikin shekaru biyu da suka gabata, nasara ta rinƙa sauya hannu tsakanin ɓangarorin biyu da ke yaƙi da juna a yankin. Dakarun Habasha da Eritrea sun kama Makelle, babban birnin yankin a watan Nuwamban 202 bayan sun zargi ƙungiyar TPLF da ƙaddamar da bore. Shekara guda bayan haka, dakarun Tigray sun ƙaddamar da harin daukar fansa a yakunan Amhara da Afar, wani abu da ya kai su kusa da Addis Ababa, babban birnin ƙasar. A baya-bayan nan kuma, dakarun Habasha da na Eritrea suna sake kame garuruwa a yankin Tigray - cikin har da birnin Shire, mai matukar muhimmanci, wanda hakan ke nuna cewa suna neman sake kama Mekelle. Alex de Waal, shugaban gidauniyar tabbatar da zaman lafiya ta duniya ya ce "Akwai aƙalla dakaru 500,000 na dakarun Eritrea da Ethiopia da ke a fagen daga, sai kuma dakaru 200,000 a ɓangaren Tigray." Ya ƙara da cewa a kiyasi an kwashe sama da kwana 50 zungur ana gwabza faɗa babu ƙaƙƙautawa, a wannan mako dakarun Tigray sun kasa ci gaba da kare kansu a garin Shire saboda ƙarancin makamai. Farfesa De Waal ya ce "Wannan babban koma-baya ne ga ƴan Tigray. Hakan ya sanya farar hula cikin haɗarin fuskantar kisan kiyashi, da fyaɗe, da kuma ƙangin yunwa", duk da cewar gwamnatin Ethiopia ta yi alƙawarin maido da layukan sadarwa a Shire da ya koma hannunta. Halin da ake ciki a Shire shi ne shaida ta irin matsalar da yankin Tigray ke ciki, inda wani ma'aikacin bayar da agaji ya ce farar hula kimanin 600,000 ne ke neman mafaka a birnin bayan guje wa yankunan da ake artabu. Mai'aikacin wanda bai son a bayyana sunansa ya shaida wa BBC cewa "Sama da mutum 120,000 ne suke zaune a filin Allah, wasu na kwana a ƙasan itatuwa ko kuma cikin dazuka". Kusan dukkanin ma'aikatan bayar da agaji sun gudu daga birnin Shire a makon jiya lokacin da dakarun Habasha suka rinka luguden wuta a kan birnin. Dubban mazauna birnin kuma suna ficewa saboda tsoron kada a ci zarafinsu - kamar yadda ta faru da mazauna wasu yankunan da suka koma ƙarƙashin dakarun Habasha da na Eritrea. Ma'aikacin jin ƙan ya ce "Wasu shaidu huɗu sun tabbatar da cewa a cikin watan Satumba an zagaye wasu mutane 46 aka yi masu kisan gilla a ƙauyen Shimblina. Mutanen ƙauyen sun tsinci gawarwakinsu cakuɗe da na dabbobi, waɗanda su ma aka kashe." Ya ƙara da cewa "Kuraye sun ci wasu daga cikin gawarwakin, an gane su ne kawai daga ragowar kayan da suka sanya. Mutanen sun ce ba su samu damar bizine gawarwakin ba, saboda haka da yiwuwar zuwa yanzu kuraye sun ƙarasa cinye su." Abin da ya sa wannan ta'asa ta yi muni shi ne mutanen da aka kashen sun fito ne daga wata ƙabila da ake kira Kunama, waɗanda ba su taɓa tsoma kansu cikin yaƙin ba. Ya ƙara da cewa "Kowane ɓangare na yin asarar dakaru, shi ya sa duk lokacin da suka shiga wani ƙauye sai su sauke fushinsu a kan ƙauyawa." Su ma dakarun Tigray ana zargin su da cin zarafi - ciki har da fyaɗe, da kisa ba bisa ƙa'ida ba, da kwasar ganima - lokacin da suka rinƙa karɓe iko a yankin Amhara da Afar, kafin dakarun gwanati su danno su baya cikin yankin na Tigray. Yankin na da al'umma da yawansu ya kai kimanin miliyan bakwai, ba su da yawa, idan aka kwatanta da yawan al'ummar ƙasar, miliyan 100. Amfani da tsohon salon yaƙi Baya ga laifukan yaƙi, ana zargin dakarun da tilasta wa fararen hula shiga yaƙi, da amfani da tsohon salon yaƙi na yin gaba-da-gaba tsakanin mayaƙa. Wani mai sharhi kan lamurran ƙusurwar Afirka da ke zaune a Birtaniya, Abdurahman Sayed ya ce "Ana ɗaukan mutane a matsayin sojoji, bayan ƴan makonni na samun horo sai a tura su fagen daga inda za su tunkari abokan gaba gaba-da-gaba." "Wannan tsohon salon yaƙi ne. Sarkin Abyssinia ne ya fara amfani da salon domin murƙushe turawan mamaye na Italiya a shekarun 1890. Duk da miyagun makaman da Italiyawan ke ɗauke da su, sai da dakarun sarkin suka ci galaba a kansu saboda yawan da suke da shi." Mr Abdurahman ya ce wannan salon yakin yana haifar da asarar rayuka masu yawa, inda ya ƙiyasta cewa an yi asarar rayuka 700,000 zuwa 800,000 a cikin shekara biyu da aka kwashe ana gwabza faɗa. Ya ƙara da cewa "wannan ne yaƙi mafi muni a tarihin ƙasar Habasha." Duk da cewa mai sharhi kan lamurran ƙasashen ƙusurwar Afirka Faisal Roble ya musanta cewa mayaƙan Tigray na amfani da tsohon salon yaki na gaba-da-gaba, ƙiyasin yawan al'umma da ya bayar bai sha banban da wannan ba. Ya ce "a ɓangarori biyu na farkon yaƙin, kimanin mayaƙa 500,000 ne suka mutu, yayin da guda 100,000 suka mutu a ɓangare na uku na yaƙin." Mr Roble ya ce mayaƙan Tigray sun samu ingantaccen horo, kuma suna yaƙin ne da zukatansu, amma dakarun Ethiopia sun fi su yawa da kuma ƙarfi a ɓangaren dabarun yaƙi ta sama. "Wani janar ɗin soji, wanda yanzu ambasada ne, ya ce za su iya ɗaukar matasa miliyan guda aikin soji a kowace shekara idan suna so, kuma suna da jiragen yaƙi da jirage mara matuƙa ƙirar Turkiyya masu inganci. Mayaƙan Tigray ba su da sojojin sama." Ya bayyana cewa sojojin sama na Habasha sun ajiye wata cibiyarsu a Asmara, babban birnin Eritrea, inda daga nan ne jiragensu na yaƙi ke tashi kasancewar ya fi kusa da yankin Tigray idan aka kwatanta da ainihin cibiyarsu da ke Bishoftu a tsakiyar Ethiopia. Mr Roble ya ce "Amma har yanzu jiragensu marasa matuƙa na tashi daga Bishoftu." Ɗaukar fansa Ƙasar Eritrea ta shiga faɗan ne kasancewar ƙungiyar TPLF tsohuwar abokiyar gabarta ce. TPLF ce take mamaye harkokin gwamnatin Ethiopia tsawon shekaru, gabanin zuwan firaminista mai ci Abiy Ahmed a 2018. Eritrea ta gwabza yaƙi da Ethiopia kan taƙaddama game da iyakar ƙasa, a lokacin da TPLF ke jagorantar gwamnatin Hasha, wani abu da ya yi sanadin rayukan mutane 80,000. Daga baya wata kotun ƙasa-da-ƙasa ta yanke hukuncin cewa Ethiopia ta miƙa wa Eritrea yankin da ake taƙaddama a kai, amma gwamnatin ta wancan lokaci ta ƙi bin umurnin kotun. An miƙa wa Eritrea yankin a watan Nuwamba na 2020, jim kaɗan bayan ɓarkewar yakin na baya-bayan nan. Masu suka na cewa shugaban Eritrea Isaias Afwerki ya sha alwashin taimaka wa Mr Abiy domin a ga bayan TPLF, saboda kada ta ci gaba da zame wa Eritrea barazana. Mr Abdurahman ya ce "Damuwar Eritrea shi ne ko dai TPLF na so ne ta sake karɓe iko a Habasha, ko kuma tana son samar da gwamnatin da ke mata biyayya a Eritrea, ta yadda za ta samu iko da gaɓar tekun Red Sea, kasancewar Tigray yanki ne da ke zagaye da ƙasashe." Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewar yayin da yaƙi ya ƙazance a yankin Tigray cikin ƴan makonnin nan, gwamnatin Eritrea ta ta ƙara ƙaimi wajen ɗaukar sojoji. A watan Satumba, bayanai sun ce dakarun Eritrea sun kai samame cikin wata coci a garin Akrur da ke kudancin ƙasar, suka tsare fasto da matasan masu ibada waɗanda suka ƙi amsa kiran gwamnati na shiga aikin soji. Farfesa De Waal ya ce wannan mataki ya nuna cewa shugaban Eritrea ba da wasa yake yi ba a wannan lamarin, sai dai bayanai na cewa bai tura matsa sabbin shiga aikin soji da yawa ba zuwa yaƙin Tigray. Ya ce "Eritrea na da dakaru a Tigray, amma a mafi yawan lokuta dakarun Habasha ne ke gwabza faɗan. Abin da Shugaba Isaias na Eritrea ke yi shi ne tsara yadda yaƙin ke gudana, saboda yana ganin cewar zai iya nuna wa Abiy hanyar samun nasara, to amma mayaƙan Tigray za su fafata, koda da wuƙake ne da duwatsu saboda a gare su lamarin tamkar na a-mutu ne ko a-yi-rai." Zai yi wahala a zauna kan teburin tattaunawa Mr Abdurahman ya ce ana gwabza yaƙin ne ta fagagen yaƙi huɗu zuwa shida, inda aka jibge dakarun Habasha da na Eritrea a kusa da garin Adigrat na yankin Tigray. Ya ce "A shirye suke su ƙaddamar da hari kan Adigrat da Mekelle." Majiyoyi daga fagen daga sun shaida wa BBC cewar dakarun sun fara dumfarar birnin Aksum ,ai ɗimbin tarihi, da Adwa da kuma Adigat daga garin Shire, inda suke nausawa daga yamma zuwa gabas. Yayin da ƙasashen duniya ke kiran a warware matsalar cikin lumana, Mr Abdurahman ya ce hakan zai yi wuya. Ya ce "Tarihi ya nuna cewa masu iko a Abyssinia, wadda ita ce Habasha a yanzu, sukan karɓe mulki ne ta amfani da ƙarfin soji. Babu mai karɓar mulki sai wanda ya fi ƙarfin dakaru. Ba su da tarihin warware rikici ta hanyar tattaunawa." Farfesa De Waal ya ce ya kamata ƙasashen duniya su hanzarta wajen tilasta a tsagaita wuta a yankin. Ya ce "Idan ba haka ba, akwai haɗarin yin kisan ƙare-dangi da kuma mace-mace sanadiyyar yunwa," yana kafa hujja da bayanan wata tawagar masana wadda a farkon shekarar nan ta yi ƙiyasin cewar farar hula na yankin Tigray sama da 250,000 ne suka mutu saboda yunwa da abubuwa makamantan haka tun bayan ɓarkewar yaƙin a 2020. "Ya kamata a ce yanzu lokacin girbi ne, amma dakaru, ƙarƙashin jagorancin Eritrea na ƙoƙarin mayar da Tigray yanki maras amfani."

Source: BBC