BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Kyautar girmamawa ta Edinburgh – Yadda Philip ya zaburar da matasa

 96877586 Gettyimages 183953399 Yarima Philip ya zaburar da matasa lokacin da ya ke raye

Tue, 13 Apr 2021 Source: BBC

In har akwai wata kungiyar da za a ce ta tasirantu da yanayin tunanin Yarima Philip, to ba ta wuce Kyautar girmamawa ta Edinburgh ba.

Tushen kyautar ya samo asali ne daga tsananin dogaro da kai, wanda ya taimaka masa yayin matsananciyar rayuwa da ya fuskanta a lokacin yarintarsa da kuma irin gogayyar da ya samu a lokacin da yake a makarantar Gordonstoun karkashin kulawar shugabanta wato Kurt Hahn.

Muhimmin abu, kamar yadda Yarima ya bayyana da kansa, shi ne "idan ka nuna wa saurayi yadda zai aiwatar da wani abu a cikin nasara, to tabbas zai sake samun nasara a wasu abubuwan da yawa.

Irin wahalhalu da kuma gwagwarmayar da Yarima Philip ya sha a lokacin da yake Gordonstoun ne suka yi sanadiyyar kafuwar yadda tsarin ya tafi.

Yarima ya yi bayanin irin kalubale da gwagwarmar da dalibai suke fuskanta a wata ganawa da BBC ta yi da shi bayan shekaru.

Ya bayyana cewa "a shekarar 1938, na tsinci kaina ina yin tafiyar mil biyar a kafa, cikin sauri a kan titinan Morayshire. Ban taba yin irin wannan tafiyar kasa ba a rayuwata kuma ba na addu'ar sake yin hakan a nan gaba."

Hakika Allah ya amsa rokona domin kuwa hakan ya haifar da samun cikakkiyar nasara, har aka kafa wannan kyauta ta girmamawa.

A 1951, bayan an yi nadin sarauniya, shi kuma fa Yarima a wannan tsarin, ba shi da wata rawar da tsarin mulki ya kebe masa, don haka, sai ya yi ta kokarin samarwa da kansa mafita.

Mr Hahn ya tuntube shi tare da neman taimakonsa domin farfado da Moray Badge. Wannan yunkuri ne ya haifar da samuwar tsarin kyautar girmamawa ta yara wanda aka fara a 1956.

John Hunt ne ya dinga bayar da kyautar gami da tsare-tsaren yadda za ta kansance. Domin mutum ne gwarzo kuma haziki, shi ne ya taba jagorantar tawagar da ta yi nasara a kan Mount Eberest, shekara ukun da suke shude.

Yadda tsarin kyautar ya taho

  • 1956: aka assasa bayar da kyautar girmamawa ta Edinburgh, bangaren yara maza.
  • 1958: an kyale yara mata shiga domin damawa da su, amma a wasu kebabbun shirye-shirye.


  • 1959: ta sami sahalewar zama kungiyar bayar da tallafi.


  • 1966: tsarin ya yadu zuwa kasashe 22.


  • 1975: Kimanin matasa miliyan daya sun shiga gasa


  • 1980: An sami daidato dangane da shigar yara maza da mata.


  • 1987: An gabatar da kyaututtuka gwal guda dubu dari.


  • 2006: Kyautar ta sami albarkaci da yarjewar masarauta a yayin bikin cikarta shekara 50.


  • 2016: Kungiya ta yi bikin shekara 60.


  • Baya ga 'yan aikace-aikace na zahiri, sabon shirin ya hadar da ayyukan tallafawa al'umma, wannan kuma ya faru ne domin a magance damuwar da Mr. Hahn yake da ita game da halin ko-in-kula a rayuwar al'umma da rashin sanin ciwon-kai a tsakanin matasa.

    Da farko sai aka fara shirin da kyaututtuka a mataki-mataki, kuma hakan ya zama wani bangaren na tafiyar da shirin.

    Wannan kungiya ba ta da wani tsari na shiga ko kayan sawa kamar irin na kungiyoyin 'yan sikawut da dai sauransa, a maimakon haka, ana ba wa duk mai son shiga damar zabar shirin da yake so a cikin tarin shirye-shirye da ake da su.

    A lokacin da kungiyar ta fara a 1956, wasu sun yi tunanin ko za ta kawo wani sauyi ne na daban, al'amarin ya kai ga ministan ilimi Sir Dabid Eccles ya taba wani subul-da-baka ya nuna kowa Yarima yana da tunanin sake kirkirar samarin Hitler.

    Da farko-farkon tsarin, an takaita shi ne kawai iya maza, wanda a wannan lokacin sama da mutum 7,000 suka shiga a watanni 12n farko.

    Amma a 1958 sai aka shigo da yara mata domin su ma a dama da su, duk da dai cewa da farko shirye-shiryensu sun bambanta da na yara maza inda aka fi mai da hankali a kan dabarun aikace-aikacen gida da kuma hidimtawa al'umma.

    Ba a bar mata sun shiga shirin dumu-dumu ba a shekarar 1965, inda kuma aka sami daidaito a tsakanin yara maza da mata a 1980.

    Gudunmawa daga bayan fage

    A farkon shekarar 1960 ne shirin ya zama gidauniyar tallafawa masu rauni. Shirin ya fadada zuwa kasashen ketare, inda aka dinga kirkirar shirye-shirye irinsa a kasashe da yawa rainon Ingila.

    A hakikanin gaskiya, Yarima bai tsaya kawai a bayan fage ba, ya shiga an dama da shi sosai a cikin al'amuran kungiyar, inda ya dinga jagorantar kwamitoci da bayar da shawarwari da kuma ba da kyaututtuka ga matasa.

    Ya kasance shugaban kwamitin amintattu har shekarar 2001, daga baya kuma ya ci gaba da kasancewa a matsayin uban kungiya.

    Matasa daga kowane lungu da sako, daga bangarori daba-daban sun shiga shirye-shiryen kungiyar, inda hakan ya tabbatar da irin nasarar da Yarima ya samu wajen jawo hankalin mutane zuwa ga kungiyar daga kowane sassa da dama na al'umma.

    Haka kuma, kungiyar ta kulla alaka da 'yan kasuwa da masana'antu wanda hakan ya ba ta damar tara isassun kudaden da ake bukata da kuma karfafa guiwar kamfanunnuka wajen karfafa kyaututtukan ga ma'aikatansu.

    A yayin da sabon karni ya tunkaro, sai aka kara fadada shirye-shiryen, inda aka shigo da masu zaman gidan kaso da kuma gidajen kangararrun yara.

    Labarin Jay

    Jay Passmore mutumin Debon ne wanda ya kasance a karkashin kulawa ta musamman tun yan dan shekara 10 sannan kuma ya ci gaba da rayuwa a karkashin kulawar mutane daban-daban.

    Ya yi rashin ji a makaranta inda aka kore shi.

    Daga nan kuma sai ya addabi mutane, har sai da 'yan sanda suka zo inda ake rike da shi domin su kama shi.

    Wuya ta sa shi dole ya sauya tunani inda da taimakon mai kula da shi, sai ya shiga wata kungiyar 'yan sa kai wadanda sun taba taimaka masa a baya.

    Sai kuma ya yanke shawarar gwada sa'arsa a kyautar girmawa ta Yarima, inda ya sami tallafin £1,500 domin biyan kudin wasu matsugunai a kauyen Zulu da ke kasar South Africa.

    Ya sami kyauta a watan Fabrairun shekarar 2013 inda daga nan sai ya ci gaba da tallafawa samari domin cimma tasu nasarar.

    A yayin gudanar bukukuwann cikar shekara 60 da samuwar kyaututtukan, Yarima ya bayyana cewa shirye-shiryen kungiyar suna ci gaba da taimaka wa al'umma kamar kullum kuma ya kara da cewa:

    "Abin lura dai lura shi ne matasa suna nan yadda suke. Amma dai yanayin da suke ciki na rayuwa ya sauya sosai, sai dai tsarin da ake bi don gane al'amuran da ke tafiya a duniya, yana nan yadda yake".

    A yayin wadannan bukukuwa, sarauniya ta yaba irin gudunmawar da wannan shiri ya bayar ga ci gaban kasa, inda ta ba da takardar amincewar masarauta da karfafa guiwa.

    Ta gaya wa majinta cewa: "Ka yi hangen nesa gami da jajircewa wajen kafa wannan kyauta ta Duke of Edinburgh shekaru 50 da suka shude."

    "Na yi matukar farin ciki da wadannan nasarori".

    Tsare-tsaren da Yarima ya samar ta wannan kungiya sun taimaka kwarai, tare da karfafa guiwoyin matasa da dama wajen samar da sababbin dabaru, tamkar yadda aka taimaka wa Philip wajen bunkasa tunaninsa a lokacin da yake karami, ba wai kawai ya tsaya iya abin da ya koyo daga aji ba.

    Ya zuwa lokacin yin bikin murnar cikar kungiyar shekaru 60 a shekarar 2016, fiye da matasa miliyan biyu da dubu dari bakwai ne a Ingila suka ci moriyar samun wannan kyauta.

    Lallai idan har wannan adadi ya ci gaba da karuwa to tabbas an taba rayuwar matasa daban-daban wajen koyar da dabaru da aikace-aikace da makamantansu.

    Akwai fitattun mutane da suka ci moriyar wannan shiri, wadanda suka hada da Dame Kelly Holmes da Ben Fogle da Richard da Peter Chambers da sauransu.

    Yarima ya kara bayyana hikimar kafa wannan shiri a wasu kalamai da ya yi a shekarar 2010, inda ya ce:

    "Daya daga cikin kalubalen rayuwar dan-adam shi ne, matasa na kowane zamani dole ne su gano yadda rayuwa take da kansu".

    Ya ci gaba da cewa "Kujiba-kujibar rayuwa na koya wa mutum darussa sannan kuma sukan nuna wa mutum cewa ana cin nasara ne a rayuwa ta hanyar kudirar aniya da hakuri da kuma jajircewa.

    Source: BBC