Menu

Liverpool da Moukoko sun kusa daidaitawa, Kane da Son na tunanin barin Tottenham saboda Conte

Liverpool Flag Logo.png Liverpool ke kan gaba cikin jerin kungiyoyin da ke rige-rigen raba Youssoufa Moukoko da kungiyarsa

Mon, 24 Oct 2022 Source: BBC

Liverpool ke kan gaba cikin jerin kungiyoyin da ke rige-rigen raba Youssoufa Moukoko da kungiyarsa. Dan wasan gaban Borusia Dortmund mai shekara 17 ya kasance dan kasar Jamus ne. (Sport, via Mail) Arsenal kuwa ta ja da baya kan kokarinta na sayen Evan Ndicka, dan Faransa kuma dan wasan bayan Einracht Frankfurt mai shekara 23, bayan da ta sabunta kwantiragin Gabriel Maghalhaes dan kasar Brazil mai shekara 24. (Express) Aston Villa za ta biya euro miliyan 10 domin nada Reuben Anorim a matsayin sabon koci, wanda a halin yanzu ke tare da Sporting Lisbon a matsayin daraktan wasanni. (Telegraph) Tsohon kocin Tottenham Tim Sherwood ya ce rashin tabbaci kan makomar kocin kungiyar mai ci Antonio Conte ne ke hana 'yan wasan gaba Harry Kane mai shekara 29 da Son Heung-min, mai shekara 30 sabunta kwantiraginsu tare da kungiyar. (Sky Sports, via Express) Chelsea na iya yi wa Hakim Ziyech, dan kasar Morocco kuma dan wasan gefe mai shekara 29 tayin komawa Juventus domin ta iya dauko Adrien Rabiot, dan wasan tsakiya mai shekara 27 daga can. (Calciomercato - in Italian) Shugaban kungiyar Ajax Edwin van der Sar ya ce ya shaida wa Arsenal cewa kungiyar ba za ta sayar da Lisandro Martinez, dan wasanta dan Argentina mai shekara 24 ba. Ya sanar da Gunners ne haka kimanin makonni kalilan gabanin dan wasan ya koma Manchester United. (Times - subscription required) Shahararren dan wasan Leicester City Gary Lineker ya ce kungiyar ta sake yin gamo da katar bayan da ta sayo Wout Faes, dan wasan baya dan kasar Belgium mai shekarun haihuwa 24. (Leicestershire Live) Dan wasan bayan Manchester United Raphael Varane mai shekara 29 na iya warkewa har ya buga wa Faransa wasanni a Gasar Cin Kofin Duniya da ke tafe a watan gobe a Qatar domin raunin da ya ji ba mai yawa ba ne. (ESPN) Tsohon dan wasan bayan Everton Jonjoe Kenny mai shekara 25 ya ce ya ki amincewa da tayin sabunta zamansa da kungiyar ta yi masa saboda a lokacin yana son barin Ingila domin ci gaba da aikinsa na kwallo a Hertha Berlin a karshen kakar wasan bara. (Liverpool Echo)

Source: BBC