Menu

La Liga: Wasu batutuwa kan wasannin mako na 27

Laliganew Za a fara wasannin La Liga daga ranar Juma'a

Fri, 31 Mar 2023 Source: BBC

Za a ci gaba da wasannin La Liga karawar mako na 27, inda za a fara wasa tun daga ranar Juma'a.

Real Mallorca ce za ta karbi bakuncin Osasuna - Osasuna tana ta taran teburi mai maki 34, ita kuwa Mallorca maki 32 ne da ita ta 11 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Ranar Lahadi Real Betis za ta ziyarci Atletico Madrid, kungiyoyin da ke fatan zama cikin 'yan hudun farko, suna son tsawaita wasa ba tare da an doke su ba a lik.

Bayan fara kakar bana da cin karo da kalubale, Diego Simone ya doke Valencia 3-0 kafin ayi hutu, kenan Atletico ta yi karawa 10 a jere ba tare da rashin nasara ba.

Kwallo hudu ne ya shiga ragar Atletico a cikin karawar 10, Antoine Griezmann ne ya kaita wannan matakin, bayan da ya koma kan ganiya.

Mai shekara 32 shine ya lashe kyautar gwarzon dan wasan La Liga a watan Maris, wanda ya ci kwallo biyu ya bayar da daya aka zura a raga a wasa uku baya.

Atletico za ta fuskanci kungiyar da ta yi wasa shida a jere ba tare da an doke ta ba a lik, koda yake Manchester United ta fitar da ita daga Europa League a bana.

To sai dai kungiyar na taka rawar gani a La Liga, wadda kwallo daya ya shiga ragarta a fafatawa uku baya.

Betis wadda take ta biyar a teburi, za ta yi fatan kammala kakar bana cikin 'yan hudun teburi, domin ta samu gurbin buga Champions League a badi.

Wani wasa da zai ja hankali masu bibiyar tamaula ranar Asabar shine wanda Barcelona za ta ziyarci Elche.

Ana sa ran kungiyar Camp Nou za ta yi nasara a karawar ta kuma bai wa Real Madrid tazarar maki 15, wadda za ta karbi bakuncin Real Valladolid ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

Wasan da Barcelona za ta kara da Elche ta karshen teburi, kamar atisaye ne kafin ta fuskanci Real Madrid a makon gobe a Copa del Rey a Camp Nou.

Barcelona wadda ta doke kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama a La Liga da ci 2-1 kafin hudu, za su kara a wasa na biyu a daf da karshe a Copa del Rey.

Barcelona ce ta ci wasan farko a Bernabeu 1-0, za a yi fafatawa ta biyu a Camp Nou, yayin da Barca ta dauki Sifanish Super Cup a kan Real a Saudi Arabia cikin Janairun 2023.

Cikin wasa hudun da manyan kungiyoyin Sifaniya suka kara daga biyar da za su yi a kakar nan, Barca ta ci uku, Real ta yi nasara 3-1 a La Liga cikin 2022.

A gasar La Liga ta kakar nan ba tabbasa tsakanin Almeria ta biyun karshen teburi da Mallorca ta 11, bayan da maki shida ne a tsakaninsu.

Kenan komai na iya faruwa a makon nan, sannan za a iya samun sauyi a matakin 'yan karshen, kuma wasu ma na son kara yin sama.

Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 68, bayan mako 26, sai Real Madrid ta biyu da maki 56, sannan Atletico ta uku da maki 51.

Wasannin mako na 27 a La Liga:

Ranar Juma'a 31 ga watan Maris

-Real Mallorca da Osasuna

Ranar Asabar 1 ga watan Afirilu

-Girona da Espanyol

-Athletic Bilbao da Getafe

-Cadiz da Sevilla

-Elche da Barcelona

Ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu

-Celta Vigo da Almeria

-Real Madrid da Real Valladolid

-Villarreal da Real Sociedad

-Atletico Madrid da Real Betis

Ranar Litinin 3 ga watan Afirilu

-Valencia da Rayo Vallecano

                        

Source: BBC