BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Lerma zai buga wa Crystal Palace tamaula kaka uku

Jefferson Lerma

Fri, 9 Jun 2023 Source: BBC

Crystal Palace ta amince da ɗaukar ɗan ƙwallon tawagar Colombia, Jefferson Lerma a kan yarjejeniyar kaka uku.

Mai shekara 28, zai koma Selhust Park ranar 1 ga watan Yuli lokacin da kwantiraginsa zai ƙare a Bournemouth.

Lerma ya sanar a Intanet ta Crystal Palace cewar ''Ina cike da murna kan samun wannan ci gaba.''

"Crystal Palace tana da fitattun 'yan wasa kuma ƙungiyar tana da kyau, zan yi ƙoƙarin bayar da gudunmuwar ci gabanta.''

Shugaban Palace, Steve Parish ya ce: ''Daukar Jefferson zai ƙara mana ƙarfin kungiyarmu, musammam ɓangaren masu buga tsakiya.''

Lerma ya koma Bournemouth a kan fam miliyan 25 daga Levante cikin watan Agustan 2018.

Ya buga wa Bournmouth wasa 184 a kaka biyar, kuma ya buga wa Colombia fafatawa 33.

Source: BBC