BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Likitoci za su yi wa Emerson na Tottenham aiki

Dan kwallon Tottenham, Emerson Royal

Tue, 28 Mar 2023 Source: BBC

Dan kwallon Tottenham, Emerson Royal na bukatar likitoci su yi masa aiki a gwiwar kafarsa.

Dan wasan ya ji rauni a lokacin da yake buga wa Brazil wasan sada zumunta a makon jiya.

Ya kuma ji raunin daf da za a tashi a wasan sada zumunta da Morocco ta doke Brazil 2-1 ranar Asabar

Tottenham na fatan dan kwallon, mai shekara 24 zai warke kafin a karkare wasannin Premier League na bana.

Emerson ya ci kwallo biyu a wasa 32 da ya yi wa Tottenham a dukkan fafatawa a kakar nan.

Ya koma kungiyar da ke Arewacin Landan da taka leda a Agustan 2021 daga Barcelona.

Tottenham wadda ke neman koci, bayan da ta kori Antonio Conte ranar Lahadi tana ta hudu a teburin Premier League.

Source: BBC