Menu

Liverpool ne manyan abokan hamayyarmu in ji Guardiola

17037010 Kocin Man City, Guardiola (hagu) da kocin Liverpool Klopp

Fri, 14 Oct 2022 Source: BBC

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce Liverpool har yanzu su ne banyan abokan hamayyarsa a tseren da ake na daukar Premier. Kungiyar da ke matsayi na goma za ta karbi bakuncin City da ke matsayi na biyu a Anfield ranar Lahadi - kuma akwai tazarar maki 13 tsakanin kungiyoyin biyu. Arsenal ce ke matsayi na daya a saman teburin kuma Conte da ke horas da Tottenham na matsayi na uku da tazarar maki uku tsakaninsa da City. Har ila yau, Guardiola ya ce Liverpool ce babbar abokiyar hamayyarsa ko da yaushe idan ana maganar cin kofi. "Idan ka tambaye ni wannan tambayar lokacin da ya rage wasa 10 kacal, zan ce ba na tunanin Liverpool za ta iya dawowa saman teburi." in ji shi. "Amma la'akari da wannan matsayi da muke, da kuma gasar cin kofin duniya, komai zai iya faruwa. "Na san karfin da suke da shi. Wasa ne da ko da yaushe yake za fi, kuma bana zaton wani abu sama da wannan." City ta yi nasara a wasanni hudu daga cikin biyar na Premier da ta buga da Liverpool, amma Liverpool ta doketa a 2019-20 da maki 18.

Source: BBC