BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Liverpool ta kai iyalan Diaz cikin birni don yin bikin Kirsimeti

68167754 Luis Diaz (tsakiya)

Sun, 19 Nov 2023 Source: BBC

Liverpool ta ɗauki mahaifan Luis Diaz da wasu iyalan cikin birnin Colombia don yin murnar bikin Kirsimeti tare.

Hakan ya biyo bayan da aka sako mahaifinsa Luis Manuel Diaz, bayan da ya yi kwana 12 a hannun masu garkuwa da mutne.

Mahaifiyar ɗan wasan Liverpool, mai shekara 26, Cilenis Marulanda tana daga cikin wadda aka ɗauke, amma aka sakota 'yan awanni tsakani.

Diaz ya haɗu da mahaifinsa a farkon makon nan a lokacin da ya je buga wa Colombia wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya.

A wani yanayi na ban tausayi, Diaz ya ci Brazil kwallo biyu a gaban mahaifinsa, wanda ya kalli fafatawar.

A shirin Liverpool na taimaka wa ɗan wasan ta ɗauki hayar jirgin sama ranar Juma'a, wanda ya kai iyalan ɗan ƙwallon Mersyside, domin su samu natsuwa, bayan fargabar da suka shiga.

Diaz zai je ya haɗu da iyalan da zarar ya kammala buga wa Colombia wasan da za ta kara da Paraguay a fafatawar neman shiga gasar cin Kofin Duniya.

Diaz bai yi wa Liverpool wasa biyu ba lokacin da aka ɗauke iyayen nasa ranar 28 ga watan Oktoba.

Source: BBC