Menu

Liverpool za ta ɗauki Mac Allister kan fam miliyan 55

Dan wasan Brighton, Alexis Mac Allister na daf da komawa Liverpool

Tue, 6 Jun 2023 Source: BBC

Dan wasan Brighton, Alexis Mac Allister na daf da komawa Liverpool kan fam miliyan 55, bayan da ƙungiyarsa ta amince ya je a gwada koshin lafiyarsa.

Dan ƙasar Argentinan, shi ne ƙashin bayan Brighton, wadda ta yi ta shida a Premier League a kakar nan.

Mai shekara 24, ya bayar da gudunmuwar da Argentina ta lashe kofin duniya a Qatar a cikin Disambar 2022.

Liverpool na fatan ƙara karfin ƙungiyar, musammam gurbin masu buga tsakiya, bayan da James Milner da Naby Keita da kuma Alex Oxlade-Chamberlain za su bar Anfield a karshen watan Yuni.

Mac Allister ya taka rawar gani da Brighton ta samu gurbin buga gasar zakarun Turai a badi ta Europa League a karon farko a tarihin ƙungiyar na shekara 122.

Ya buga wasa 40 da cin kwallo 12, yawancin a gurbin lamba 10 a fili, wasu lokutan ya kan zama tsani tsakanin masu tsaron baya da masu cin kwallaye.

Mac Allister ya koma Brighton daga ƙungiyar Argentinos Juniors a Janairun 2019, daga nan aka bayar da aronsa a ƙungiyar ta Buenos Aires.

Ya fara yi wa Brighton wasa a karawar da ta tashi ba ci da Wolverhampton Wanderers a Maris din 2020 - kawo yanzu ya yi wasa 112 da cin kwallo 20 a ƙungiyar.

Mac Allister ya buga wa tawagar Argentina wasa 16, ya kuma yi wasa shida a gasar kofin duniya da Argentina ta lashe kofin a 2022.

Ya kuma ci kwallo a wasan da Argentina ta ci Poland a fafatawar cikin rukuni a wasannin da Qatar ta karbi baƙunci.

Source: BBC