BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Liverpool za ta saurari masu zawarci Matip, Mourinho na son koma wa Chelsea

Joel Matip

Mon, 6 Feb 2023 Source: BBC

Liverpool za ta saurari tayin da aka gabatar ma ta kan dan wasanta mai shekara 3, kuma tsohon mai takawa Kamaru kwallo Joel Matip. Kwantiraginsa ba zai kare a Anfield ba sai 2024. (Football Insider)

Ana hasashen babu mamaki mai horar da West Brom Carlos Corberan, dan shekaru 39, ya maye gurbin Jesse Marsch a Leeds United. (Mail)

Tsohon kocin Chelsea Jose Mourinho na son koma wa Stamford Bridge a karo na uku, kuma dan asalin Portugal din mai shekara 60, ya tuntubi masu sha'awarar sayan kungiyar lokacin da aka sa ta a kasuwa. (GiveMesport)

Akwai yiwuwar Chelsea ta nuna bukatar hayan kocin Sifaniya mai shekara 52, Luis Enrique, 52, idan ta yanke hukunci maye gurbin mai horar da kungiyar a yanzu Graham Potter. (Fichajes - in Spanish)

Barcelona na bibbiya ko sa ido kan dan wasan Gabon da ke buga gaba a Chelsea Pierre-Emerick Aubameyang, yayinda suke kitsa yadda za su dawo da dan wasan mai shekara 33, Camp Nou . (Football Transfers)

Newcastle United za ta ci gaba da nuna zawarci kan dan wasan Ingila mai shekara 22, da ke buga tsakiya Conor Gallagher bayan tattaunawa da Chelsea kan saye shi a Janairu. (Football Insider)

Liverpool da Aston Villa sun nuna zawarcinsu kan dan wasan Athletic Bilbao asalin Sifaniya Nico Williams, mai shekara 20, da kuma dan wasan tsakiya Oihan Sancet, shi ma mai shekaru 22. (AS via Teamtalk)

Daraktan wasanni a Bayern Munich Hasan Salihamidzic ya ce fitar da yuro miliyan 70 kan dan wasan Manchester City Joao Cancelo a matsayin dan wasan aro, zai yi wa kulob din wahala. (Mirror)

Dan wasan Brazil mai shekaru 30 da ke buga tsakiya Philippe Coutinho, na cikin 'yan wasa da ake alakantawa da tafiya zaman aro a Galatasaray bayan fama da Aston Villa a wannan kaka. (Sun)

Daraktan wasanni a Paris St-Germain, Luis Campos ya tabbatar da cewa kungiyar na tattaunawa da dan wasan Argentina da ya lashe kofin duniya Lionel Messi, mai shekara 35, kan sabon kwantiragi. (Mail)

Source: BBC