0
MenuAfrica
BBC

Lucas Vazquez ya gama buga wa Real wasannin bana

Tue, 13 Apr 2021 Source: bbc.com

Dan kwallon Real Madrid, Lucas Vazquez ya yi rauni, kuma watakila zai yi jinya har zuwa karshen kakar bana.

Real ce ta bayyana hakan ta kuma ce ya yi rauni ne a wasan hamayya na El Clasico da ta doke Barcelona 2-1 ranar Asabar.

Vazquez wanda ke tsaron baya daga gefen hagu, bayan da Dani Carvajal ke jinya, ya yi taho mu gama da dan kwallon Barcelona Sergio Busquests da ta kai ya yi raunin.

Mai tsaron bayan shi ne ya bai wa Karim Benzema kwallon farko da ya zura a raga Barcelona, inda Real ta ci wasa na shida a jere a dukkan fafatawa da ta buga kwanan nan.

Valquez ya yi wa Real karawar da ta doke Liverpool 3-1 a gasar Champions League wasan farko a daf da na kusa da na karshe ranar Talata.

Sai dai ana sa ran Alvaro Odriozola ne zai maye gurbinsa a wasa na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai da za su buga a Anfield ranar Laraba.

Source: bbc.com