Menu

Man Utd na son sauya Joao Felix da Ronaldo, Villa na neman wanda zai maye gurbin Gerrard

23848005 Cristiano Ronaldo

Mon, 24 Oct 2022 Source: BBC

Manchester United na nazari kan kyale Cristiano Ronaldo ya bar kungiyar a kyauta bayan da kocin kungiyar ya ajiye dan wasan gaban dan kasar Portugal mai shekara 37 a benci bayan da yaki shiga ya buga wasa yayin da aka umarce shi yayi haka a wasan da Red Devils suka kara da Tottenham ranar Laraba. (The i) Ana sa ran Red Devils za su kai samame kan Joao Feliz, dan wasan gaban Atletico Madrid mai shekara 22, wanda shi ma dan Portugal ne, domin ya maye gurbin Ronaldo. (Deportes Cuatro - in Spanish) Kocin Sporting Lisbon Ruben Amorim na cikin jerin sunayen masu horas da wasan kwallo da Aston Villa ta zana domin maye gurbin Steven Gerrard, sai dai tsohon koci Tottenham Mauricio Pochettino ba shi da sha'awar karbar aikin. (The Athletic - subscription required) Tsohon kocin Chesea Thomas Tuchel ma ba ya sha'awar karbar ragamar kungiyar ta Aston Villa. (Telegraph) Sai dai idan Villa na son dauko Amorim, tilas ta biya kungiyarsa euro miliyan 30 kafin ta sako shi, wanda tarin kudi ne da ba kasafai akan sami haka ba a duniya. (Mirror) Arsenal na sha'awar dauko Evan Ndicka, dan wasan baya dan kungiyar Eintracht Frankfurt ta Jamus mai shekara 23. (Evening Standard) Wakilin Erling Haaland dan wasan gaba na Manchester City mai shekara 22 ya yi murna da labarin da k eyawo cewa dan wasan zai sanya hannu kan wata sabon kwantiragi da kungiyar. (90min) Chelsea da Liverpool da kuma Manchester United dukkansu a shirye suke su raba Frankie de Jong, dan Netherlands, kuma dan wasan tsakiya mai shekara 25 daga kungiyarsa ta Barcelona. (ESPN)

Source: BBC