Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Mali ya bukaci da a gaggauta saki kuma ba tare da wani sharadi ba, Shugaba Bah Ndaw da kuma Firaministan kasar Moctar Ouane bayan rahotannin da ke cewa sojoji sun kama tare da tsare su a wani bariki.
A wani sakon Twitter, hukumar Majalisar Dinkin Duniyar, Minusma ta kuma yi kira da a kwantar da hankali a kasar ta Yammacin Afirka da ke fama da rashin kwanciyar hankali.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran sakamakon rudani da rashin tabbas da aka shiga bayan da rahotanni ke cewa an ga sojoji sun yi gaba da shugaban rikon-kwarya Bah Ndaw tare da Firaministansa Moctar Ouane, zuwa sansanin soji na Kati da ke kusa da babban birnin kasar Bamako.
Rahotanni sun ce shi ma Ministan Tsaro Souleymane Doucouré na tsare a hannun sojojin.
Labarin ya sa ana rade-radi da fargabar cewa wani juyin mulki ne na biyu aka sake yi a cikin shekkara daya a kasar da ke yankin yammacin Afirka.
Lamarin ya kasance ne bayan a jiya Litinin din Firaministan ta wani kiran gaggawa da ya yi ta waya da kamfanin dillancin labarai na AFP yake cewa sojoji sun je domin su kama shi. Kamfanin dillancin labaran y ace, iya abin da suka iya ji daga MIsta OUane ke nan sai kawai layin wayar tasa ya katse.
Kungiyar Tarayyar Afirka, AU, da kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO, da Kungiyar Tarayyar Turai, EU da kuma Amurka dukkaninsu sun yi Allah-wadarai da kama shugabannin, suna gargadi da kiran sojojin da su gaggauta sakin manyan 'yan siyasar na Mali, ba tare da wani sharadi ba.
Rahoton kamen ya kasance ne 'yan sa'o'i bayan wani gyaran fuska da aka yi a gwamnatin rikon-kwarya ta kasar ta Mali, inda aka sauya wasu manyan sojoji biyu da suka taka rawa a juyin mulkin shekarar da ta gabata.
Wasu majiyoyi sun sheda wa BBC cewa sojojin da suka kama shugabannin ba su ji dadin cire hafsoshin biyu ba shi ya sa suka dauki wannan mataki domin nuna bacin ransu, tare da neman a mayar da su kan mukamansu na ministoci. Sannan kuma sun nemi Moctar Ouane ya sauka daga mukaminsa.
Wani lokaci a baya sojojin na Mali da ke da lakabin M5, wadanda suka taka rawa sosai wajen hambarar da gwamnatin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita sun bukaci da a rushe gwamnatin rkon-kwaryar.
Mali dai a ce ta kara fada wa yanayi na rashin tabbas, watanni tara bayan juyin mlkin sojin da ya raba Shugaba Ibrahim Boubakar Keïta da iko.
Juyin mulkin da yawancin 'yan kasar suka yi maraba da shi, amma kuma jama'ar suka nuna fushi da bacin ransu kan yadda sojoji suka kankane gwamnatin rikon kwarya da ta biyo baya da kuma tafiyar hawainiya da sabbin hukumomin kasar ke yi wajen aiwatar da sauye-sauyen da suka yi alkawari.
Alkawarin gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a watan Fabrairu na 2022 a kasar, da mayar da ita tsarin mulkin dumokuradiyya a farkon shekara mai zuwa za su kasance wani abu da zai yi wuya ya tabbata.
Yankin gaba daya na matukar bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Mali, wanda hakan ne zai iya dakatar da bazuwar ta'annatin masu ikirarin jihadi
Wani juyin mulkin da aka yi a baya a shekara ta 2012 ya sa mayaka masu ikirarin jihadi, ribatar yanayin rashin kwanciyar hankali, inda suka kwace yankuna a arewacin kasar ta Mali.
Duk da yake sojojin Faransa da ke jibge a kasar sun taimaka wajen kwato yankunan, amma kuma mayakan sun ci gaba da kai hare-hare.
Ana bayyana aikin tabbatar da zaman lafiya da dakarun Majalisar Dinkin Duniya ke yi a kasar ta Mali da cewa shi ne mafi hadari a duniya. Kusan sojojin Majalisar 250 suka rasa ransu a can tun shekara ta 2013.