BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ma'aikatan Najeriya sun shiga tasku lokacin mulkin Buhari - NLC

16328510 Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya

Thu, 4 May 2023 Source: BBC

Hukumar Ƙwadago ta Najeriya ta ce ma'aikatan ƙasar na cikin wani hali, kuma babu wani sauyin a zo a gani da aka samu tun bayan kama mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

A wata tattaunawa da BBC, albarkacin ranar ƙwadago ta duniya, sakataren ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, Kwamared Nasir Kabir ya ce ci gaba kaɗan ne kawai za a iya cewa ma'aikata sun samu a ƙarƙashin gwamnati mai ci.

Ya ce "abin farin ciki ne sake zagayowar ranar ma'aikata ta duniya, amma maganar gaskiya al'amuran da ma'aikata (a Najeriya) suke ciki da abubuwan da suke fama da su ba abin murna ko farin ciki ba ne."

Abubuwan da ya bayyana cewa su ne manyan ƙalubalen da ma'aikata a Najeriya ke fuskanta su ne:

  • Tashin farashin kayan masarufi
  • Rashin isassun kuɗi a hannu


  • Biyan kuɗin makarantar yara


  • Tsadar wutar lantarki


  • Tsadar man fetur
  • Kuɗin kiwon lafiya


  • A cewar kwamared Nasir ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya ba zai ishi magidanci ya sayi buhun shinkafa da zai ciyar da iyalansa ba.

    A cewarsa "idan ka duba a halin yanzu ma'aikaci a Najeriya na cikin hali ne na lahaula."

    A lokacin da aka tambaye shi ko ma'aikata sun samu ci gaba ƙarƙashin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, sai ya ce "ban da ci baya, babu abin da ma'aikata suka gani."

    'Wuri ɗaya tilo da aka samu ci gaba'

    Kwamared Nasir ya ce wuri ɗaya tilo kawai da ma'aikata suka samu ci gaba a lokacin mulkin shugaba Buhari shi ne batun biyan albashi.

    Ya ce "abu ɗaya wanda muka gani wanda shi ne za mu iya cewa za mu yaba wa wannan gwamnati shi ne maganar biyan albashi."

    "Da gaske sun biya albashi kuma suna biya babu tsaiko, amma maganar gaskiya ita ce albashin bai taka kara ya karya ba tunda ba ya isan ma'aikata," in ji shi.

    'Muna yi wa gwamnati mai zuwa kyakkyawan zato'

    Kwamared Nasir ya ce kowace gwamnati da irin tsarin da takan zo da shi, kuma suna sa ran gwamnatin da za a rantsar ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu za ta ɗauki matakin kyautata wa ma'aikata.

    Sai dai ya ce ƙungiyar ta NLC ba za ta ƙyale ba idan ta ga cewa gwamnatin ba ta yin abin da ya kamata wajen inganta rayuwar ma'aikata.

    Source: BBC