Liverpool ta kammala sayen ɗan ƙwallon Argentina, Alexis Mac Allister a kan kuɗi fam miliyan 35 daga Brighton.
Ɗan ƙwallon ya sanya hannu a yarjejeniyar shekara biyar.
Ya taimaka wa Brighton wajen samun gurbi a Gasar Europa da za a buga a kakar wasa mai zuwa.
Ɗan shekara 24, Mac Allister ya zura ƙwallo 20 a wasa 112 da ya buga wa Brighton, sannan ya taimaka wa Argentina lashe Kofin Duniya a bara.
"Mafarkina ya zama gaskiya, na zaƙu na fara murza leda," in ji Mac Allister.
Kocin Liverpool Jurgen Klopp na ƙoƙarin ƙara ƙarfin tawagarsa sakamakon ficewar 'yan wasan tsakiya irinsu James Milner, Naby Keita da Alex Oxlade-Chamberlain.
Mac Allister ya koma Brighton ne daga ƙungiyar Argentinos Juniors a watan Janairun 2019.