Menu

Maguire ne gwarzon ɗan wasan Premier na watan Nuwamba

Maguire Leicester United Harry Maguire

Fri, 8 Dec 2023 Source: BBC

Kocin Manchester United Erik ten Hag da ɗan bayan ƙungiyar Harry Maguire sun lashe kyautar koci da ɗan wasan da suka fi ƙoƙari a watan Nuwamba.

United ta yi rashin nasara a wasa huɗu cikin bakwai na farko da ta buga a Premeir a wannan kakar amma tun daga nan ta koma ta shida a saman teburi.

Sun ci wasanni uku da suka buga a watan Nuwamba ba tare da an zira musu ko ƙwallo guda ba - wasan da suka buga da Fulham da na Luton sai kuma na Everton.

Maguire wanda ya yi ta fama da suka a farkon wannan kakar, ya buga duka wasanni ukun ba tare da an sauya shi ba.

Dan wasan mai shekara 30 shi ne ɗan bayan ƙungiyar na farko da ya lashe wannan kyauta tun bayan Nemanja Vidic da ya lashe ta a Janairun 2009.

"Ba zan iya yin hakan ba, ba tare da taimakon abokan wasana ba, ma'aikatanmu da kuma magoya baya. Muna sane da nuna ƙauna da goyon bayan da kuke mana, muna farin ciki," kamar yadda Maguire ya rubuta a shafinsa na X bayan ya karɓi kyautar.

Kocin United Ten Hag ya ƙalubalanci kokarin Maguire a watan Yuli, inda ɗan wasan ya fara tunanin barin Old Trafford, gabanin a fara kakar nan.

Kazalika, ya yi watsi da tayin da ya samu daga West Ham ya ci gaba da zama a United, duk da cewa ƙungiyar tasa ta amince da tayin da aka yi mata na yuro miliyan 30 kan ɗan bayan.

Ya zarce 'yan wasa shida da aka fitar da sunayensu ciki har da ɗan wasan Manchester City, Jeremy Doku, da Anthony Gordon na Newcastle da mai tsaron ragar Luton Thomas Kaminski da Raheem Sterling daga Chelsea sai kuma ɗan wasan Bournemouth Marcus Tavernier.

Source: BBC