BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Mai yiwuwa ne burin Najeriya na samun gagarumar bunƙasar arziƙi nan da 2050?

Nigerian Flag 3.png Experts in Nigeria have started commenting on the national development plan

Thu, 4 May 2023 Source: BBC

Masana a Najeriya sun fara tsokaci game da shirin raya ƙasa da ake sa ran zai kawo wa ƙasar gagarumin ci gaban tattalin arziƙi nan da shekara ta 2050.

Shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado ne ya ƙaddamar da sabon shirin raya ƙasar ranar Laraba.

Ana sa ran shirin zai taimaka wajen bunƙasa arziƙin da ƙasar ke da shi, da kashi bakwai cikin 100 tare da samar da guraben aiki ga ƴan Najeriya miliyan 165.

Wasu masana a Najeriya sun shaida wa BBC cewa duk da shirin raya ƙasar, abu ne mai matuƙar kyawu, sai dai yana fuskantar ɗumbin ƙalubale ciki kuwa har da batun cewa ya zo a makare.

An ƙaddamar da shirin ne kusan mako bakwai bayan majalisar zartarwar Najeriya ta amince da shi a ranar 15 ga watan Maris.

Shirin mai taken Ajandar Najeriya ta 2050 yana da burin ganin mutum zai iya samun kuɗin shiga jimillar $33,328, kwatankwacin naira miliyan 15 a shekara.

Matakin dai idan ya tabbata, zai sanya Najeriya shiga cikin ƙasashen duniya masu matsakaicin samun kuɗin shiga.

Haka zalika, shirin yana da burin samar da wani tattalin arziƙi mai taƙama da ilmi, da ke bunƙasa, ga kuma haɓakar masana'antu da za su dama da kowa, kuma ya kawo ci gaba mai ɗorewa ga ƙasar.

Yayin ƙaddamar da shirin a fadar Aso Rock, an ambato Shugaba Buhari yana cewa idan za ku iya tunawa a watan Maris ɗin 2020, na amince a ɓullo da shirye-shiryen raya ƙasa da za su gaji Burin Najeriya 20:2020 da kuma Shirin Bunƙasawa da Farfaɗo da Tattalin Arziƙi daga 2017 - 2020.

Shirye-shiryen duk sun gama aiki a watan Disamban 2020, in ji Buhari.

Sabon shirin raya ƙasar da ya gaje su, na da burin bunƙasa samar da ayyukan yi daga miliyan 46.49 a 2020, zuwa jimillar miliyan 203.41 a 2050.

A wata zantawa da BBC, Farfesa Garba Ibrahim Sheka, masanin tattalin arziki a Najeriya ya ce shirin abu ne mai kyau idan aka duba abubuwan da aka tsara nufin cimmawa.

"Duk da dai ba a fitar da shi gaba ɗayansa ba, amma shiri ne mai kyau wanda zai kawo ci gaban tattalin arziƙi na ƙasa a waɗannan shekaru da suka ɗiba wato daga nan zuwa 2050." in ji masanin.

A cewarsa, tsarin ya zo da sabon abu, kasancewar ya shigar da mutane da yawa daga fannoni daban-daban wajen tsara shi.

Saɓanin "a ce ofisoshi su zauna, su rubuta abin da za su rubuta, a wannan karon an nemi masu masana'antu da ƙungiyoyin matasa da ƙungiyoyin mutane masu buƙata ta musamman duka an sanya ra'ayoyinsu a cikin tsarin."

Shi kuwa, Dakta Murtala Muhammad Adoge, ƙwararre kan sha'anin tsare-tsare na cewa ƙasashe irinsu Indiya da Bangladesh a nahiyar Asiya, da Ghana da Rwanda a Afirka duk suna yin irin waɗannan tsare-tsaren raya ƙasa.

Sai dai ya ce babbar matsalar da ake samu a Najeriya ita ce yawan sauyin gwamnati.

Ya ce babban burin da ke ƙunshe cikin wannan shiri, shi ne samar wa mutane kimanin miliyan 200 aikin yi.

Sai dai, in ji shi, nan da shekara 27 mai zuwa a ƙarshen wannan shirin raya ƙasa, yawan al’ummar Najeriya zai ƙaru zuwa miliyan 400, don haka ko gwamnati ta yi nasarar cimma ƙudurin samar wa mutum miliyan 200 aiki, to “sauran miliyan 200 fa?” ya tambaya.

'Shirin raya ƙasa na dogon zango ya fi wuya'

A cewar Farfesa Sheka, Najeriya ƙasa ce da kasafin kuɗin shekara-shekara ma ba a iya aiwatar da shi sosai - nasarar aiwatar da kasafin kuɗin sai a ce ba ta fi kashi 30% ko kashi 40% ba.

Ya ce "Idan tsari na gajeren zango yana ba mu wahala, a tarihin ƙasar nan, tsari na dogon zango shi ya fi bayar da wahala, domin tsari irin wannan.

Tsari ne wanda za ka tsaya a nutse, ka hango nesa, ka gano me za ka samu - kuɗaɗen da kake samu, ta ina za su ƙaru? Me za ka yi su ƙaru? Idan sun ƙaru kuma me za ka yi, ka bunƙasa tattalin arziƙi nan da shekara 10 zuwa 15 zuwa shekara 20?"

Ya ba da misali da ƙasashen da suka ci gaba kamar Isra'ila - inda ya ce wani lokacin suna da shirin raya ƙasa na shekara 70.

"Wannan tsarin da ake yi na gine-ginen gidaje a ɓangaren Palasɗinu duk yana ciki. Duk shugaban ƙasar da ya zo, sai dai ya ɗora a kan wannan.

Wani ya gama, wani ya ɗora".

Masanin ya ce a Najeriya ba irin haka ake yi ba.

Farfesa Sheka ya ce tsare-tsaren baya da suka ruguje, an ɗora su ne a kan hasashe na kuɗin shiga daga man fetur, kuma hasashen a shekara ɗaya ma sai a ce za a sayar da mai ganga a kan dala 70, amma sai a ga ta dawo dala 20 ko dala 30 daga nan sai kasafin kuɗi ya ruguje.

Dakta Murtala Muhammad Adoge, ya ce yawan al’ummar Najeriya na ƙaruwa cikin sauri kuma yawan haihuwar da ake ya kai kashi 3.6% duk shekara.

Farfesa Sheka ya ƙara da cewa: "Abin da ba mu iya hasaso shi (daidai) a shekara ɗaya ba, ina za a hasaso shi a shekara 20 ko 30?" Farfesa Sheka ya tambaya.

A cewarsa, irin wannan tsari yana buƙatar ya kasance abin da aka yi yau, ya zama ya tallafawa na gobe, abin da za a yi gobe, ya tallafa wa na jibi, kuma hakan na faruwa ne idan akwai kishin ƙasa.

Babu rashawa da cin hanci saboda duk kyawun tsari, idan akwai rashawa sai ka ga tsarin bai tafi daidai ba," in ji Farfesa Sheka.

'Shirin ya zo a makare'

Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce duk da yake, shirin raya ƙasa na 2050 abu ne mai kyau, amma kuma ya zo a makare kasancewar Shugaba Buhari ya samu shekara takwas a kan mulki.

"Ya kamata a ce a shekara ta biyu ko ta uku ya fara dasa shi, yanzu kawai tsara shi aka yi a takarda, kuma aka ajiye, ana sa ran gwamnati mai zuwa, ta zo ta yi aiki da shi,

"Kuma tabbas ne gwamnati mai zuwa za ta samu shirin bai yi mata daidai ba domin tana da nata tsare-tsare na daban, za ta iya ɗaukan wasu abubuwan daga ciki amma ba zai yiwu ta ɗauke shi gaba ɗaya ta ci gaba da aiki da shi ba."

Ya ce Najeriya a bisa al'ada, ba a cika samun gwamnati mai ɗorawa a kan ayyukan gwamnatin da ta gada ba.

"Kowa da irin tsarinsa, musamman idan an yi magana kan tsaro da ci gaban tattalin arziƙi waɗanda su ne a iya cewa ƙalubale na wannan gwamnati.

Kuma sabuwar gwamnati za ta zo da nata shirin na cewar ga yadda za ta yi, ta bunƙasa ƙasa ga kuma yadda za ta yi ta kawo tsaro, ba lallai ba ne ta ɗauki shirin da wannan gwamnati ta tsara ba.

Shi ma Dakta Murtala Adoge ga alama ya yi amanna da wannan ra'ayi, inda ya ƙara da cewa: “A Najeriya, za a yi wannan tsari (na raya ƙasa) kuma shugaba na gaba zai zo, sai ya ga tsarin bai yi masa ba gaba ɗaya, don haka sai ya tattara aikin ya ajiye a gefe

Daga nan sai ya fara tunanin ƙirƙiro nasa, saboda idan ya yi nasara a ce shi ne ya yi.” In ji masanin tsare-tsaren.

Zai yi wuya a iya cimma ƙudurorin tsarin nan kusa...

Game da yiwuwar cimma ƙudurorin da aka zayyana a tsarin ta yadda Najeriya za ta iya gogayya da ƙasashe masu matsakaicin samun kuɗin shiga, Farfesa Sheka ya ce da kamar wuya.

Saboda "abin da aka fito fili aka nuna shi ne ana sa ran rashin aikin yi zai ragu daga yanayin da yake ciki na kashi 33.3 cikin 100 ya dawo kashi shida.

Ya ce hakan ba ƙaramin gagarumin aiki ba ne don kuwa a kundin tsarin, ana tsammanin mafi yawan ayyukan yi za su zo ne daga ɓangaren kamfanoni.

"Ya nuna cewar sai an yi aiki tuƙuru wajen samar da ingantaccen yanayi ga kamfanonin da za su zo su kafa harkokinsu, ya zamo suna cin riba." in ji shi.

Ya kuma ce a halin da ake ciki, da yawan kamfanoni rufewa suke yi saboda tsadar kayan sarrafawa da hauhawar farashi, "wannan ta sa kasuwa ta durƙushe, mutane ba sa iya sayen kayayyaki saboda abubuwa sun yi tsada."

A bayaninsa, Farfesa Sheka ya ce babban abu ne a ce babbar matsalar da ake ciki a Najeriya ta rashin aikin yi, wanda ya kai kashi 33.3%, kawai ya faɗo ƙasa zuwa kashi 6.3%.

Masanin ya yi tsokaci kan yadda Najeriya a ƴan shekarun nan ke fuskantar koma-baya a maimakon samun ci gaba.

"Gwamnati ba ta da kuɗaɗe, sai a ce a ranto, kai hatta kasafin kuɗin da ake yi, sai an ranto," in ji Sheka.

"Kuma yanayi na bunƙasa masana'antu ya haɗar da matakan da gwamnati ta fara ɗauka na gina ababen more rayuwa kamar shimfiɗa layin jirgin ƙasa wanda duk masana'antun da suka dogara da kayan sarrafawa daga waje, zai zo ta jiragen ruwa,"

"Daga nan za a ɗauke shi zuwa Kaduna ko Sokoto, wannan yana ƙara tsadar abubuwa saboda hanyar da ake tafiyar da su, wato titin mota ta yi tsada, jirgin ƙasa ko jirgin ruwa shi ne mai arha, amma babu hanyoyin da za su kai su, kuma gwamnati ba ta ƙarasa ba.

Game da ƙudurin rage fatara a Najeriya kamar yadda tsarin ya bayyana, Farfesa Sheka ya bayyana cewa mutum sama da miliyan 83 cikin miliyan 200 suna cikin talauci - kashi 80 na yan Najeriya ke nan.

Ya ce burin tsarin shi ne talaucin ya faɗo ya zama kashi 2.1% na mutanen Najeriya ne kawai suke cikin fatara.

A cewarsa, mafarki ne kawai wanda an rubuta shi ne, ba lalle a iya cimma hakan ba.

"Idan aka ce fatara ana nufin wanda ba zai iya samar wa kansa abubuwan more rayuwa ba, musamman abinci ko ruwan sha, ko kuma idan ba shi da lafiya ya je asibiti ko ɗinka nagartaccen tufafi da sauransu." kamar yadda masanin ya ce.

Me ake nufi da ƙasa mai matsakaicin samu?

Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce ƙasar da ake kira mai matsakaicin samu, ita ce wadda ba talaka ba ce futuk kuma ba mai arziƙi ba ce.

Idan aka ce mutum na da matsakaicin arziƙi, ya fi ƙarfin abin duniya - abincin da zai ci da abin walwala duk ya fi ƙarfinsu, amma kuma idan ka kalle shi ba za a ce mai arziƙi ba ne.

"Ƙasashe manya irinsu Amurka da Faransa da Ingila, da sauran ƙasashen Turawa su ne ƙasashe masu haɓakar tattalin arziki waɗanda mutanensu mafi yawa suna cikin yalwa.

Akwai kuma ƙasashe masu fatara sosai kamar Burkina Faso da ƙasashen da suke Afirka ta Yamma irinsu Chadi.

A cewarsa, matsakaitan ƙasashe su ne waɗanda suka fi ƙarfin abubuwan da suke bai wa mutane wahala, kuma akwai ayyukan yi, akwai bunƙasar tattalin arziki amma ba su kai na manyan ƙasashe ba.

Masanin ya bayyana cewa kashi 75 cikin 100 na ƙasashen duniya suna matakin matsakaicin samu, sauran kuma kashi 25 cikin 100 akwai masu arziƙi kuma akwai matalauta futuk.

Ya ake gane ƙasa mai matsakaicin samu ce?

Masanin tattalin arzikin ya ce akwai matakin da ƙasashe ke takawa su kasance cikin rukunin masu matsakaicin samu shi ne bunƙasar tattalin arziƙi kamar daga kashi uku zuwa biyar a shekara.

Sai dai ya ce hakan na da alaƙa da yawan mutanen ƙasa.

"Kuɗin da Najeriya take samu, zai iya fin na wata ƙasar da ake ganin ta taka matakin 'higher middle income' amma saboda su ƴan kaɗan ne. Shi ya sa da wuya a kwatanta su.

Yawancin mutane za ka ji ana kwatanta Saudiyya da Najeriya - Saudiyya su miliyan 30 ne da 'yar ɗoriya, Najeriya kuma ana zancen miliyan 200, in ji Farfesa Sheka.

"Kuma abin da muke sayarwa mu samu kuɗi, Saudiyya ta fi mu shi,

Idan da Saudiyya za ta samu kuɗi daidai da na Najeriya, duk da haka sai sun fi mu jin daɗi da walwala,"

"Domin kuɗin da za su samu, za a raba ne kan mutum miliyan 30, mu kuma kuɗin da za mu samu idan ya yi daidai da na Saudiyya za a raba shi a kan mutum miliyan 200."

"Idan ka raba shi 'per capita' za ka ga cewa, mu za mu iya faɗawa matakin 'low middle income' su kuma za su iya shiga matakin 'high income'.

Mataki na biyu da ƙasashen za su taka shi ne taƙaita yawan al'umma.

Misali idan aka bari kamar yadda yake a Najeriya, yawan al'umma na ƙaruwa kuma arzikin ƙasa (harkar noma da masana'antu) ba sa haɓaka, za a shiga rikici abinci bai isa ba, aikin yi bai isa ba, wanda kuma wannan matsala muke fuskanta a yanzu." in ji shi.

Ya ce idan haɓakar al'ummar ƙasa ta haɗu da ƙwazon neman jama'a kamar China ko Indiya, sai a riƙa samun ci gaba.

"Domin mutanen suna da ilmi, kuma suna da ƙwarewa, suna ba da gudunmawa ga tattalin arziƙi.

Amma idan haɓakar tattalin arziƙin ta kasance taron yuyuyu ce, in ji masanin sai dai almajirai da cima-zaune, sai a ga, ga yawa amma ba shi da amfani."

Source: BBC