Manchester City na zawarcin dan wasan tsakiyar West Ham Lucas Paqueta.
Dan kasar Brazil ya koma Hammers ne daga Lyon kan fan miliyan 36.5 a bazarar da ta wuce kuma ya taka rawar gani yayin da kungiyar ta lashe gasar cin kofin Europa.
Mai yiyuwa ne Man City ta gwada kudurin West Ham yayin da Pep Guardiola ke neman karfafa ‘yan wasansa bayan nasarar da suka samu a kakar wasa da ta gabata inda su ka lashe manya gasanni guda uku.
West Ham za ta yi jinkirin rasa wani babban jigo a cikin tawagar David Moyes bayan ficewar Declan Rice zuwa Arsenal kan fan miliyan 105.
Paqueta na da shekaru hudu a kan kwantairagin da ya sanya hannu a kai a bazarar da ta gabata.
Idan ta dauko Paqueta, City za ta iya amfani da Bernardo Silva a matsayin dan wasan gefen dama - kamar yadda ta yi akai-akai a karshen kakar wasan da ta gabata.
Phil Foden kuma zai iya taka leda a wannan bangaren, tare da Paqueta za su bai wa City zaɓi mai yawa a tsakiya, bayan Kevin de Bruyne da Julian Alvarez da kuma Mateo Kovacic da aka ɗauko a wannan bazara .