Menu

Man City na bibiyar Ferguson, watakil Mbappe ya je Liverpool

Evan Ferguson

Wed, 6 Sep 2023 Source: BBC

Manchester City na sa ido kan ɗan wasan Brighton Evan Ferguson mai shekara 18, inda take da yaƙinin ɗan ƙasar Jamhuriyar Ireland zai dawo garesu domin su haska tare da Erling Haaland. (inews)

Ana raɗe-raɗin ɗan wasan gaba a Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 24, na duba yiwuwar tafiyar Liverpool a kaka mai zuwa yayinda ya ke kokarin ganin ya bar PSG a 2024. (L'Equipe - in French, subscription required)

Manchester United na tattaunawa kan tsawaita zaman ɗan wasanta na baya Aaron Wan-Bissaka bayan matashin mai shekara 25 ya burge kocinsa Erik ten Hag da nasarori a kakar da ta gabata. (Telegraph - subscription required)

Liverpool ta so musayan ɗan wasan Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 24, da ɗan wasan Portugal mai buga gefe Joao Felix a wannan kaka, amma ɗan wasan mai shekara 23 ya yi watsi da tayin, da kuma wadda Manchester United da Aston Villa suka gabatar. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Manyan mutane biyu da ke sahun gaba a neman saye Manchester United sun ce an gaya musu za a jaye batun sayar da ƙungiyar duk da faɗuwar darajar ƙungiyar da fan miliyan 600. (Mail)

Ɗan wasan gaba a Chelsea da Ingila Raheem Sterling, mai shekara 28, ya ce ba zai yi ritaya daga bugawa ƙasarsa ba, duk da cewa kocinsu Gareth Southgates na ware shi. (Telegraph - subscription required)

Ana saran mai bugawa Everton kuma asalin ƙasar Jamaica Demarai Gray, mai shekara 27, zai yi bankwana da ƙungiyar zuwa Saudiyya a yarjajeniyar shekara hudu da ƙungiyar Al-Ettifaq da Steven Gerrard ke horarwa. (Fabrizio Romano)

West Ham na fafatawa da ƙungiyoyi Turkiyya irinsu Galatasaray da Fenerbahce a kokarin saye Jesse Lingard mai shekara 30 daga Manchester United. (Football Insider)

Ɗan wasan tsakiya a Denmark Jesper Lindstrom, mai shekara 23, ya yi watsi da tayin fan miliyan 25 daga Eintracht Frankfurt zuwa Liverpool, inda ya yanke hukuncin tafiya Napoli saboda a ganinsa zai fi samun dama a gasar Serie A. (Tipsbladet - in Danish)

Chelsea na son ɗan wasan baya Ian Maatsen ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsawon lokaci a Stamford Bridge, bayan ɗan wasan mai shekara 21 ya yi watsi da tayin fan miliyan31 da ya samu daga tsohuwar ƙungiyar da ya yi zaman aro Burnely. (Fabrizio Romano)

Wakilin Jorginho ya ce ɗan wasan na Italiya mai shekara 31 da ke buga tsakiya midfielder, zai zauna a Arsenal duk da kwaɗayin da ƙungiyar Fenerbahce ta Turkiyya ke nunawa. (Tutto Mercato - in Italian)

Ɗan ƙasar Faransa Christophe Galtier, mai shekara 57, da Paris St-Germain ta kora a watan Yuli in July duk da lashe Ligue 1, na shirin maye gurbin Hernan Crespo a matsayin kocin kungiyar Al-Duhail ta Qatar. (RMC Sport - in French)

Source: BBC