BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Man City na neman tabbaci daga Bellingham kafin ta saye shi, Barca da Inter za su yi musaya

Jude Bellingham

Mon, 17 Apr 2023 Source: BBC

Manchester City na dab da cimma nasarar sayen dan wasan Borussia Dortmund Jude Bellingham sai dai tana son samun tabbaci daga matashin dan wasan tsakiyar na Ingila mai shekara 19 cewa zai yarda ya zauna a karkashin Pep Guardiola. (Sunday Mirror)

Brighton ta yi wa dan wasanta na tsakiya Alexis Mac Allister farashin fam miliyan 60 zuwa 70, amma kuma tana ma sa ran samun abin da ya fi haka kasancewar Chelsea da Liverpool da Manchester United dukkaninsu na son. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Faransa Aurelien Tchouameni na fafutukar samun gurbi a jerin 'yan wasan farko na Real Madrid amma kuma kungiyar ba ta ma tunanin sayar da matashin mai shekara. (AS)

Kociyan Barcelona Xavi ya ce ba ya tunanin cewa Gavi zai ji dadin tafiya wata kungiya ya ji dadi duk da cewa ana danganta matashin dan Sifaniyar mai shekara 18 da Chelsea. (90min)

Barcelona da Inter Milan sun gana domin tattaunawa a kan musayar 'yan wasa, inda Franck Kessie na Ivory Coast zai bar kungiyar ta Sifaniya zuwa Inter, yayin da Marcelo Brozovic na Croatia zai je Barcan. (Gazzetta dello Sport )

Chelsea ba ta da niyyar sayar da dan wasanta na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 Levi Colwill, wanda yake zaman aro a Brighton, kuma dan bayan mai shekara 20 zai kasance cikin wadanda kungiyar ke son yin amfani da su a kaka mai zuwa. (Independent)

Tottenham ta fara tattaunawa da dan bayanta na Ingila Eric Dier, domin kulla yarjejeniyar shekara uku da shi wato har zuwa 2026, kuma tana son a gaggauta kammala maganar kafin, ya yin da take shirin daukar sabon kociya. (Football Insider)

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp zai bar Joel Matip na Kamaru ya bar kungiyar a bazara. (Football Insider)

Newcastle United ba za ta sabunta kwantiraginta da Allan Saint-Maximin ba kuma a shirye take ta saurari tayi daga kungiyoyi a kan dan gaban na gefe dan Faransa. (Teamtalk)

RB Leipzig na sha'awar matashin dan wasan gaba na Arsenal Folarin Balogun, mai shekara 21, wanda ya taka rawar gani a zaman aro a Reims, kuma kungiyar ta Jamus tana son amfani da shi domin maye gurbin Christopher Nkunku, na Faransa wanda zai tafi Chelsea a bazara. (Todofichajes)

Tsohon kociyan Crystal Palace Patrick Vieira ne na farko a cikin wadanda Nottingham Forest ke son dauka idan har ta rabu da Steve Cooper. (Daily Star)

Source: BBC