Sheffield United ta yi rashin nasara da ci 2-1 a gida a hannun Manchester City a wasan mako na uku a Premier League ranar Lahadi.
Kungiyoyin biyu sun kammala zagayen farko ba tare da cin kwallo a raga ba.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Erling Haaland ya ci kwallon farko, amma kuma Jayden Bogle ya farke, saura minti biyar a tashi wasan.
To sai dai City ta samu maki ukun da take buƙata bayan da Rodrigo Hernandez ya zura na biyu a raga, saura minti biyu lokaci ya cika.
City ta buga karawar ba tare da kociyanta Pep Guardiola ba, wanda aka yi masa aiki da ba zai ja ragamar karawa biyu ba a jere.
Ranar 2 ga watan Satumba, City za ta karbi bakuncin Fulham a karawar mako na hudu a Premier League.
Kungiyar da ke Etihad ta fara da cin Burnley 3-0 ranar 12 ga watan Agusta da fara kakar bana, sannan ta yi nasara a kan Newcastle United da ci 1-0 ranar 19 ga watan Agusta.