BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Man United na zawarcin Kane, Barcelona na son Aubameyang

Harry Kane

Tue, 25 Apr 2023 Source: BBC

Manchester United na ci gaba da kokarin sayo dan wasan tsakiya na Tottenham Hotspur Harry Kane a kakar nan, ya yin da kyatin din Ingilar mai shekaru 29 ke sa ran rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya a kulub dinsa. (The Telegraph)

Eagles ta yi wa dan wasan Crystal Palace kuma na gaban Ivory Coast Wilfried Zaha tayin sabon kwantiragin fam miliyan 200 a duk mako. Mai shekaru 30 din zai kasance a kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a karshen kakar nan idan kwantiraginsa ya kare. kungiyoyin Arsenal, da Chelsea Paris St-Germain na cikin masu zawarcinsa . (Guardian)

AC Milan ta sanya kudi fam miliyan 35 domin sayo mai tsaron ragar Kamaru Andre Onana, ya yin da ita ma Chelsea ke zawarcin dan wasan mai shekara 27. (Goal)

Mai kai hari na Chelsea Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 33, Na daga cikin gagarumin aikin da Barcelona ta sanya ido a Nou Camp a wannan kakar, amma duk da haka ta yi dabara kebe dan wasan Poland Robert Lewandowski idan wancan cinikin bai fada ba (Sky Sports)

Dan wasan gaba na Liverpool Roberto Firmino, mai shekara 31, na son komawa Barcelona idan kwantiraginsa ya kare a karshen kakar nan, sai dai kuma kulub din na Sifaniya baya sha'awar daukar dan wasan na Brazil.(Marca)

Newcastle United da Borussia na cikin kungiyoyin da suke sanya ido kan dan wasan Leeds Crysencio Summerville, mai shekara 21 tare da fatan za su yi nasara kan dan wasan. (Football Insider)

Chelsea na gab da kammala yarjejeniyar daukar dan wasan tsakiya na Portugal Diego Moreira, mai shekara 18, in da za su dauko shi daga Benfica. (90min)

Newcastle da Manchester United su ma na zawarcin dan wasan gaba na Slovenia Benjamin Sesko, matashin dan wasan shekararsa19, ya na kuma taka leda a Red Bull Salzburg a karshen mako. (90min)

Liverpool da Chelsea sun bi sahun Manchester City a kokaqwar dauko matashin dan wasan baya na Croatia Vuskovic mai shekara 16, su na kokarin dauko shi daga Hajduk Split. (Daily Mail)

Arsenal na duba yiwuwar sake shiga kasuwar sayan dan wasan Wolves, kuma na gaban Portugal, Pedro Neto, mai shekara 23. (TeamTalk)

Source: BBC