BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Man United ta amince da tayin sayen Onana kan fam miliyan 47.2 daga Inter

Andre Onana

Fri, 21 Jul 2023 Source: BBC

Manchester United ta amince da tayin fam miliyan 47.2 domin sayen Andre Onana mai tsaron ragar, Inter Milan.

Kungiyar ta Old Trafford za ta biya fam miliyan 43.8 wajen sayen mai tsaron ragar tawagar Kamaru da karin fam miliyan 3.4 na tsarabe-tsarabe.

United na fatan dan kwallon mai shekara 27 zai je Amurka don buga wa United wasannin atisaye da za ta buga don tunkarar kaka mai zuwwa, amma sai an nemar masa takardar izinin zuwa kasar.

Kocin United, Erik ten Hag ya bukaci a sayo masa dan wasan a karshen kakar da ta wuce, wanda ya horar da golan a Ajax.

Kocin na ganin golan zai taimakawa United a wasannin kakar 2022, hakan ya sa David de Gea ya zabi barin United, bayan da aka bukaci ya tsawaita zamanssa.

Onana ya yi kaka bakwai da rabi a Ajax, daga nan ya koma Inter a Yulin 2022.

Ya yi wasa takwas kwallo bai shiga ragarsa ba a karawa 24 a Serie A, yayin da Inter ta kammala a mataki na uku a teburin babbar gasar Italiya.

Haka kuma ya yi wasa 13 a Champions League da kwallo bai shiga ragarsa ba a fafatawa takwas, inda Inter ta yi ta biyu a gasar, bayan da Manchester City ta lashe kofin.

Onana shine na biyu da United ta dauka a bana kenan, bayan sayen Mason Mount daga Chelsea kan fam miliyan 55.

Source: BBC