Manchester United ta sanar da 'yan wasan da za su buga mata wasannin gasar Champions League kakar 2023/24 kamar yadda Uefa ta wallafa.
United tana rukunin farko da ya hada da Bayern Munich da FC Copenhagen da kuma Galatasaray.
Kungiyar Old Trafford za ta fara da ziyartar Bayern Munich a Allianz Arena ranar 20 ga watan Satumba.
United ta bayyana 'yan wasa 25 da ya kunshin fitattun 'yan kwallon da take ji da su da waɗanda kungiyar ta horar ko suke da alaka da ita.
Haka kuma kafin ta buga karawa da kungiyar Jamus za ta kara sanar da wasu rukunin 'yan wasan da zai hada da Alejandro Garnacho da wasu 'yan kwallon daga makarantar koyon tamaula ta United.
Kungiyar ta Old Trafford ta yi wa dukkkan 'yan wasan da ta saya a baya rigistar buga gasar Zakarun Turai har da Sofyan Amrabat da Rasmus Hojlund, wanda zai fuskanci tsohuwar ƙungiyarsa ta Copenhagen.
Sai dai 'yan wasan da aka fitar, waɗanda za su buga karawar cikin rukuni ne daga baya za a ƙara wasu daga matasan ƙungiyar.
'Yan wasan da United ta yi wa rijistar buga Champions League: