0
MenuAfrica
BBC

Man United ta ci gaba da zama ta biyu a teburin Premier

Tue, 13 Apr 2021 Source: bbc.com

Manchester United ta je ta doke Tottenham da ci 3-1 a wasan mako na 31 a gasar Premier League da suka fafata ranar Lahadi.

Edison Cavani ne ya fara cin kwallo a ragar Tottenham daga baya aka soke ta, bayan da aka ce Scott McTominay ya doki Son Heung-min a fuska kafin ya bayar da tamaular.

Daga nan kuma Son ya ci wa Tottenham kwallo saura minti biyar alkalin wasa ya umarci 'yan kwallon su yi hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Fred ya farke, bayan da Cavani ya nemi golan Tottenham, Hugo Lloris wanda ya yi amai.

Daga baya ne Cavani ya kara ta biyu a wasan, sannan Greenwood ya ci na uku da hakan United ta hada maki ukun da take bukata.

Da wannan sakamakon United tana ta biyu a kan teburi da tazarar maki 11 tsakaninta da Manchester City wadda ke jan ragama.

Ita kuwa Tottenham ta ci gaba da zama a mataki na bakwai da tazarar maki shida tsakaninta da West Ham United wadda take ta hudu a teburi Premier League a bana.

Source: bbc.com