Menu

Man United ta ci wasan sada zumunta karo na biyu a jere

Yan wasan Manchester United

Wed, 19 Jul 2023 Source: BBC

Manchester United ta doke Lyon da ci 1-0 a wasan sada zumunta don tunkarar kakar da za a fara ta bana cikin watan Agusta.

United wadda za ta buga Champions League a kakar nan, bayan da ta kare a mataki na uku a Premier League da ta wuce ta ci kwallon ta hannun Donny van de Beek.

Wasan sada zumunta na biyu da ta yi nasara kenan bayan cin Leeds United 2-0 ranar Laraba 12 ga watan Yuli.

Wadanda suka ci wa United kwallayen sun hada da Noam Emeran da kuma Joe Hugill.

Kawo yanzu United ta dauki Mason Mount daga Chelsea ta kuma amince da tayin sayen mai tsaron ragar Inter Milan, Andre Onana.

Golan tawagar Kamaru ya tsare ragar Ajax kaka bakwai da rabi karkashin Erik ten Hag daga nan ya koma Inter Milan.

Sauran wasannin sada zumunda da United za ta buga:

Asabar 22 ga watan Yulin 2023

  • Manchester United da Arsenal


  • Laraba 26 ga watan Yulin 2023

  • Manchester United da Wrexham


  • Monday 31 ga watan Yulin 2023

  • Manchester United da Borussia Dortmund
  • Asabar 5 ga watan Yulin 2023

  • Manchester United da Lens


  • Lahadi 6 ga watan Yulin 2023

  • Manchester United da Athletic Bilbao


  • Source: BBC