Manchester United ta sayi golan Turkiyya Altay Bayindir daga Fenerbahce kan kudi fan miliyan 4.3.
Dan wasan mai shekara 25, wanda ya buga wa kasarsa wasanni biyar, zai koma kan kwantiragin shekaru hudu.
A kakar wasan da ta wuce ya kasance babban dan wasa a Fenerbahce yayin da ta lashe kofin Turkiyya kuma ta zo ta biyu a gasar Super Lig.
Sayen Bayindir ya biyo bayan ficewar mai tsaron gida Dean Henderson, wanda ya koma Crystal Palace ranar Alhamis kan kudi fan miliyan 20.
Bayindir ya zama mai tsaron gida na biyu da ya koma United a bana bayan ta sayi dan kasar Kamaru Andre Onana daga Inter Milan kan fam miliyan 47.2.
Ya shafe kaka biyar a Fenerbahce bayan ya koma daga takwararta ta Turkiyya Ankaragucu a shekara ta 2019, inda ya buga wasanni 166.