Arsenal ta kusa kammala daukar dan wasan West Ham kuma dan wasan tsakiyar Ingila Declan Rice mai shekara 24 a kan fan miliyan 100. (Guardian)
Mai horar da ‘yan wasan Manchester Pep Guardiola, na shirin barin kungiyar bayan kwantiraginsa ta kare a 2025. (Guardian)
Kungiyar RB Leipzig na son akalla fam miliyan 75 idan har Manchester City na son siyan dan wasan bayan Croatia Josco Gvardiol mai shekara 21. (Talksport)
Manchester City ta yi watsi da tayin Paris st-German na hadawa da dan wasan tsakiyar Italiya Marco Verreatti da kuma mai tsaron ragar Italiya Gianluigi Donnarumma, a bangaren yarjejeniyar da za a sanya hannu ta siyan dan wasan Portugal Bernardo Silva. (Footmercato – French)
Arsenal na fargabar cewa Chelsea za ta iya shan gabanta wajen daukar dan wasan tsakiyar Brighton Moises Caicedo ta hanyar kara masa albashin da ya fi wanda Arsenal din za ta ba shi. (Football Transfers)
Mai tsaron ragar Kamaru Andre Onana, shi ne wanda Chelsea ke son dauka a matsayin mai tsaron ragarta, yayin da Inter Milan kuma ke son a ba ta fam miliyan 50 a kan dan wasan. (Evening Standard)
Manchester United na ci gaba da tattaunawa da Chelsea a kan dan wasan tsakiyar Ingila Mason Mount, to amma har yanzu ba a daidaita ba a kan cinikin. (Sky Sports)
Bisa ga dukkan alamu da wuya Manchester United ta ci gaba da neman dan gaban Tottenham Harry Kane, saboda Tottenham ba ta son sayar da kyaftin din Ingila, musamman ga wata kungiya ta Firimiya. (Sky Sports)
Tottenham ta shirya tuntubar Brentford don tattaunawa a kan farashin mai tsaron ragar Spaniya David Raya.
To sai dai kuma Tottenham da kuma wadanda ke son dan wasan ba sa son su biya fam miliyan 40 a kansa. . (Sky Sports)
Newcastle United na shirin taya dan wasan tsakiya na Wolfsburg, Felix Nmecha mai shekara 22, wanda ake kyautata tsammanin farashinsa zai kusa kai wa fan miliyan 15, sannan kuma tana duba yiwuwar daukar dan wasan tsakiyar Nice Khephren Thuram mai shekara 22. (Telegraph )