BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Man Utd na tsaka-mai-wuya a kan gola, Enrique na son Silva

David de Gea

Sun, 2 Jul 2023 Source: BBC

Dole sai Manchester United ta sayar da 'yan wasa kafin ta iya sayen mai tsaron ragar Kamaru Andre Onana, mai shekara 27, da ke kungiyar Inter Milan.(Talksport)

A dangane da hakan ne United ta bukaci David de Gea, wanda kwantiraginsa ya kare ba da jimawa ba a Old Trafford da kada ya tafi wata kungiyar, ko da za su kasa samun wanda zai maye gurbinsa a iya kudin da suke da shi a kasafinsu. (Sun)

Chelsea ta amince ta bar Cesar Azpilicueta, ya tafi Atletico Madrid a kyauta ba tare da wani kwantiragi a kansa ba. (Marca )

Haka kuma Chelsean ta kusa cimma yarjejeniya da Inter Milan ta barin Romelu Lukaku, ya koma can dindindin daga aro. (90min)

Luis Enrique zai bayar da fifiko kan neman sayen dan wasan Manchester City na Portugal Bernardo Silva, idan ya maye gurbin Christophe Galtier a matsayin kociyan Paris St-Germain coach. (90min)

Sannan tsohon kociyan na Sifaniya yana kuma son PSG ta sayo Joao Felix, daga Atletico Madrid. (Relevo )

Manchester United na son sayen dan gaban Porto Mehdi Taremi, dan Iran mai shekara 30. (Jornal de Noticias )

Kociyan Roma Jose Mourinho na son ganin ya sayo dan wasan tsakiya na Brazil Fred daga tsohuwar kungiyarsa Manchester United. (Sun)

Dan wasan Chelsea Christian Pulisic ya cimma yarjejeniya ta baka kan dogon kwantiragi da AC Milan, to amma har yanzu kungiyoyin biyu ba su cimma matsaya a kan kudin tafiyar dan wasan na Amurka ba. (ESPN)

Maganar tafiyar Hakim Ziyech na Chelsea zuwa Al Nassr ta Saudiyya ta gamu da cikas bayan da dan wasan na Moroko ya kasa tsallake gwajin lafiyarsa da aka yi. (Mail)

A dangane da haka aka gabatar wa da Ziyech din sabuwar yarjejeniya tare da rage yawan albashinsa da kashi 40 cikin dari, amma shi kuma ya ki yarda. (CBS)

Chelsea za ta kara azama wajen ganin ta yi nasarar sayen dan wasan tsakiya na Ecuador Moises Caicedo, mai shekara 21, inda take sa ran Brighton za ta amince da tayinta na fam miliyan 80. (Standard)

Fulham na neman fam miliyan 60 a kan dan wasanta na tsakiya dan Portugal Joao Palhinha, idan West Ham na sonshi, wanda kudi ne da Hammers din ba su taba kashewa ba a sayen dan wasa. (Football Insider)

Kazalika West Ham din ta yi nisa a tattaunawa da Leicester City a kan cinikin dan wasan gaba na Ingila Harvey Barnes. (90min)

Fam miliyan 65 kadai zai rage wa Manchester United ta sayi wani sabon dan wasan gaba idan har ta kammala cinikin Mason Mount, na Chelsea. (Mail)

Watakila sai Bayer Leverkusen ta kara farashi idan har tana son Arsenal ta sayar mata da Granit Xhaka. (Mirror)

Matashin dan wasan gaba na Brazil Angelo Gabriel, mai shekara 18, ya kammala kasin farko na gwajin lafiyarsa domin tafiya Chelsea daga Santos a kwantiragin shekara shida. (Fabrizio Romano)

Sannan kuma Chelsean ta bai wa Levi Colwill sabon kwantiragi. (Standard)

Wakilin Marc Cucurella ya yi watsi tare da bayyana rahoton da jaridar Sifaniya Marca ta yi cewa Chelsea ta yi wa Atletico Madrid tayin dan wasan, a matsayin labarin karya. (Metro)

Willian ya yi watsi da tayin karin shekara daya da Fulham ta yi masa, yayin da tsohon dan wasan na Brazil ke kokarin samun tayi daga wasu kungiyoyin na Premier. (Standard)

Har yanzu dan bayan Fulham Tosin Adarabioyo, dan Ingila shi ne na gaba-gaba da Tottenham ke son saye a bazaran nan. (Football London)

Manchester City za ta bar Zack Steffen ya tafi a bazaran nan, inda Leicester City kuma ke nuna sha'awarta a a kan mai tsaron ragar dan Amurka. (ESPN)

Dan bayan Slovakia Milan Skriniar, na shirin tafiya Paris St-Germain a kyauta idan kwantiraginsa ya kare da Milan. (Goal)

Source: BBC