BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Man Utd ta kayyaɗe kuɗin sayen Mount, Arsenal tayi fintinkau a cinikin Rice

Mason Mount

Mon, 12 Jun 2023 Source: BBC

Ɗan wasan tsakiya a Chelsea da Ingila Mason Mount, mai shekara 24, ya kasance wanda Manchester United ke bai wa fifiko a wannan kaka, amma kungiyar ta ce ba za ta biya sama da fam miliyan 60 a kansa ba. (Givemesport)

Newcastle United na son gabatar da tayi mai kwabi kan dan wasan RB Leipzig da ke buga tsakiya, Dominik Szoboszlai, mai shekara 22. (L'Equipe, via Sport Witness)

Manchester United ta nuna damuwa kan shirinta na sayo dan wasan Koriya ta Kudu daga Napoli Kim Min-jae, mai shekara 26, muddin Harry Maguire ya kin amincewa da yarjejeniyar barin Old Trafford. (90min)

Arsenal na kan gaba a cinikin ɗan wasan West Ham kuma Kyeftin Declan Rice, mai shekara 24, sai dai har yanzu ba ta kai makuran kudin da kungiyarsa ke nema a kansa ba. (90min)

West Ham tuni ta soma nazarin dauko dan wasan Fulham da Portugal Joao Palhinha, mai shekara 27, domin maye gurbin Rice. (talkSPORT)

Manchester United na kokarin zabtare kudin da ake nema kan mai tsaron raga Diogo Costa, sai dai kungiyarsa ta Porto ta dage kan dole a biya fam miliyan 75. (Abola - in Portuguese)

Everton ta shiga rukunnin masu farautar dan wasan Coventry Viktor Gyokeres, mai shekara 25, amma tana fuskantar kalubale daga West Ham, Wolves, Fulham, Leeds, Southampton da Sporting Libson. (Abola - in Portuguese)

Dan wasan Borussia Monchengladbach da aka kiyatsa kudinsa kan fam miliyan 30 Manu Kone, 22, na cikin 'yan wasan da Liverpool ke farauta. (Sky Sports Germany, via Inside Futbol)

Bayer Leverkusen na son fam miliyan 40 kan Jeremie Frimpong, mai shekara 22 a wannan kaka, sai dai babu mamaki kudin ya sanyaya gwiwar masu zawarcinsa irinsu Manchester United. (Metro)

Aston Villa da Tottenham na zawarcin ɗan wasan Italiya Nicolo Zaniolo mai shekara 23 daga Galatasaray, amma akwai kalubale da ga kungiyoyi irinsu Juventus da AC Milan. (Tuttojuve.com)

Ɗan wasan Colombian Yerry Mina mai shekara 28, ba zai je Besiktas ba idan kwantiraginsa a Everton ya kare, kasancewa kungiyar ta Turkiyya ba ta da niyyar cika yarjejeniyar da aka bukata kan dan wasan. (Fanatik)

Liverpool ta kasance inda a yanzu zai fi dacewa da matashin dan wasan Bayern Munich da Faransa Benjamin Pavard mai shekara 27 da ke neman kungiyar sauya sheka. (CaughtOffside)

Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya ce yana son cimma yarjejeniya da dan wasan Paris St-Germain da Faransa Kylian Mbappe mai shekara 24, amma ba a wannan shekarar ba. (Madrid Xtra, via 90 min)

Arsenal ta amince da yarjejeniyar kwantiragin shekara hudu kan dan wasan Faransa mai shekara 22 William Saliba. (The Athletic)

Wolverhampton Wanderers na zawarcin dan wasan Southampton James Ward-Prowse, bayan kungiyarsu ta fada rukunni dagaji a Championship. (Givemesport)

Source: BBC