BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Man Utd ta nace wa Phillips, Ibrahimovic zai koma Milan

90710913 Dan wasan Ingila Jadon Sancho

Mon, 11 Dec 2023 Source: BBC

Ɗan wasan tsakiya na Manchester City da Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 28, na cikin ƴan wasan farko da Manchester United za ta yi cefane. (Sun)

Manchester United na sa ido kan ɗan wasan gaba na RB Leipzig da Belgium Lois Openda, mai shekara 23, a yayin da ƙungiyar ke neman wanda zai maye gurbin ɗan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 23 da ɗan wasan gaba na Faransa Anthony Martial, mai shekara 28. (Mirror)

Newcastle na nazarin karɓo ɗan golan Crystal Palace Sam Johnstone, mai shekara 30. (Star)

Manchester City na son ɗauko ɗan wasan gaba na Club Brugge Tajon Buchanan a Janairu amma sai ta biya fam miliyan 50 kafin karɓo ɗan wasan na Canada. (Star)

Newcastle United na shirin karɓo aron ƴan wasa daga Saudiyya a Janairu. (Football Insider)

Shugaban Barcelona Joan Laporta na shirin tattaunawa kan makomar ƴan wasan Portugal Joao Felix, mai shekara 24, da kungiyar ta karɓo aro daga Atletico Madrid, da Joao Cancelo, mai shekara 29, da ta karɓo aro daga Manchester City. (Sport - in Spanish)

Manchester United ta sha gaban Tottenham kan buƙatar ɗan wasan Nice mai shekara 23 Jean-Clair Todibo. (Football Insider)

Everton ta yi watsi da buƙatar Tottenham na sauya yarjejeniyar da suka amince ta fam miliyan 10 kan ɗan wasan Ingila Dele Alli, mai shekara 27, zuwa Goodison Park a Janairun 2022. (Times - subscription required)

Matashin ɗan wasan Reading mai shekara 18 Caylan Vickers na fatan cika burinsa na buga wa Real Madrid ƙwallo. (Sun)

Manchester United ta tuntuɓi Stuttgart kan ɗan wasan gaba na Guinea Serhou Guirassy, mai shekara 27 wanda za ta iya karɓa ƙasa da farashin fam miliyan 20. (Sky Sports Germany)

Bayern Munich ta saka ɗan wasan baya na Barcelona Ronald Araujo, mai shekara 24, cikin jerin ƴan wasan da take farauta. (Sky Sports Germany)

Tsohon ɗan wasan gaba na Sweden Zlatan Ibrahimovic, wanda ya yi ritaya daga taka leda a kakar da ta gabata, ya ce yana tattaunawa da AC Milan kan dawo wa ƙungiyar. (Sky Sports Italia, via Football Italia)

Source: BBC