Menu

Man Utd za ta riƙe Lindelof, Barcelona na son Greenwood

59326063 Victor Lindelof

Mon, 1 Jan 2024 Source: BBC

Manchester United za ta tsawaita kwantiragin ɗan wasan bayanta na Sweden Victor Lindelof har zuwa watan Yuni na 2025. A tsarin kwantiraginsa na baya zai ƙare ne a lokacin bazaran nan. (Athletic )

Haka kuma Manchester United ɗin ta shirya karɓar tayi daga masu son sayen ɗan bayanta na Faransa Raphael Varane a watan Janairu. (Football Insider)

Tottenham za ta gabatar da tayin sayen ɗan wasan bayan Genoa Radu Dragusin, kuma ɗan Romaniyar mai shekara 21 na sha'awar komawa ƙungiyar ta London in ji wakilansa. (SportItalia daga Standard)

Spurs ɗin sun mayar da hankalinta kan Dragusin ne saboda tattaunawar da suke yi kan cinikin ɗan bayan Nice Jean-Clair Todibo, na dab da wargajewa. (Fabrizio Romano)

Wataƙila kociyan Juventus Max Allegri ya hana cinikin da ƙungiyar ke yi na sayen Kalvin Phillips daga Manchester City saboda ba ya ganin ɗan wasan na tsakiya na Ingila ya dace da tsarinsa. (Calciomercato - in Italian)

Wataƙila Barcelona za ta fasa sayen Mason Greenwood saboda a halin yanzu ba za ta iya sayen matashin ɗan wasan gaba na Manchester United wanda ke zaman aro a Getafe ba kan farashin fam miliyan 40. (Sport )

Tuni Atletico Madrid ta mika buƙatarta ta sayen Greenwood. (Marca)

Brentford za ta gabatar da tayin sayen ɗan wasan gaba na gefe na Real Betis Assane Diao a kan kuɗin da ya kusa yuro miliyan 30, na sharaɗin sayen matashin na Sifaniya mai shekara 18. (Diario de Sevilla daga Sport Witness)

Newcastle za ta soke aron da ta bayar da Issac Hayden ga Standard Liege, kuma ƙungiyoyin Ingila da dama na ƙasa da gasar Premier na sha'awar ɗan wasan na tsakiya. (Football Insider)

Borussia Dortmund na sha'awar sayen ɗan bayan Chelsea Ian Maatsen na Netherlands a watan Janairu. (Voetbal international)

Everton na sa ido a kan matashin ɗan wasan tsakiya na Manchester City, Alex Robertson na Australiya mai shekara 20, wanda a yanzu yake zaman aro a Portsmouth. (The News)

Nottingham Forest na fatan kammala cinikin fam miliyan 6 a kan matashin ɗan wasan Fluminense Nino a farkon Janairu kuma tuni tattaunawa ta yi nisa da Monaco a kan sayen ɗan Portugal Gelson Martins. (Mirror)

Source: BBC