Newscastle United na sa ido kan Dominic Calvert-Lewin na Everton da ɗan wasan na Ingila mai shekara 26 ke cikin ƴan wasan da ƙungiyar ke farauta idan an buɗe kasuwar cinikin ƴan wasa. (TeamTalk)
Fulham ta shiga hamayya da Liverpool da Manchester United kan ɗan wasan tsakiya na Fluminense mai shekara 22 na Brazil Andre, yayin da kuma take harin ɗan wasan Denmark da ke taka leda a Wolfsburg mai shekara 24. (Standard)
Manchester United na shirin zubin sabbin ƴan wasa a 2024 inda za ta raba gari da ƴan wasanta 10 a hunturu da bazara. (MEN)
Kusan ƴan wasa 15 za su bar United, ciki har da ɗan wasan gaba na Ingila Jadon Sancho, da ake sa ran zai tafi a farkon shekara. (Star)
Manchester City na ƙoƙarin shawo kan Erling Haaland, mai shekara 23, ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya. (TeamTalk)
Chelsea na sa ido kan dan wasan Mexico na Feyenoord Santiago Gimenez, mai shekara 22, da ɗan wasan Real Betis ɗan ƙasar Senegal Assane Diao, mai shekara 18, a kasuwar cinikin ƴan wasa ta Janairu. (FootballTransfers)
Arsenal ta yanke shawarar sayen ɗan wasan gaba a 2024 - amma kuma sai a bazara. (Football Insider)
Arsenal da ɗan wasan tsakiya na Italiya Jorginho ba su sasanta ba kan sabuwar yarjejeniya, a cewar wakilin ɗan wasan mai shekara 31. (Mail)
Tottenham na harin karbo ɗan wasan Club America Sebastian Caceres ɗan ƙasar Uraguay mai shekara 24 a watan Janairu. (Football.London)
AC Milan na son karɓo aron ɗan wasan Chelsea mai shekara 22 ɗan ƙasar Faransa Benoit Badiashile, yayin da ƙungiyar ke shawarar tuntuɓar Arsenal kan ɗan wasan baya na Poland Jakub Kiwior, mai shekara 23. (Calciomercato - in Italian)
Chelsea za ta saka ɗan wasan baya na Ingila Trevoh Chalobah, kasuwa. (Football.London)