Manchester United sun shirya tsaf domin dauko dan wasan tsakiya na Ingila da West Ham Declan Rice mai shekara 24, sai dai har yanzu ana ganin Arsenal na ci gaba da matsawa domin daukar dan wasan. (Guardian)
Dan wasan Marseille kuma na tsakiyar Faransa Matteo Guendouzi, mai shekara 24, ka iya maye gurbin Rice a West Ham.(Mirror)
Chelsea da Manchester United na zawarcin dan wasan Aston Villa kuma golan Argentina Emiliano Martinez, dan shekara 30, a wani bangaren kuma ana rade-radin ita ma kungiyar Tottenham ita ma ta na neman sabon mai tsaron raga. (Mirror)
Chelsea za ta bari mai tsaron gida na Brazil Thiago Silva mai shekara 38 ya sake komawa taka leda a Fluminense a wannan kakar. (Telegraph - subscription)
Manchester United ta fara tattaunawa da mai tsaron baya na Koriya ta Kudu, kuma mai taka leda a Napoli Kim Min-jae. Baya ga wannan su ma kungiyoyin Liverpool da Paris St-Germain sun nuna sha'awa kan dan wasan mai shekara 26. (Foot Mercato - in French)
Ana sa ran Tottenham su karkare batun dauko dan wasan gaba na Sweden Dejan Kulusevski, mai shekara 23, daga Juventus a kakar nan. (PA via Independent)
Arsenal na sha'awar dauko dan wasan RB Leipzig mai shekara 23, Mohamed Simakan wanda shi ne mai tsaron ragar Faransa, kuma kwantiraginsa zai kare a watan Disamba ma izuwa. (Guardian)
Dole ne kungiyoyin Tottenham da Manchester United su biya fam miliyan 40, idan su na son daukar mai tsaron ragar Sifaniya David Raya, mai shekara 27, daga Brentford a kakar nan. (Evening Standard)
Newcastle ka iya sanya fam miliyan 30 kan sayo dan wasan Bayer Leverkusen, kuma na gaban Faransa Amine Adli mai shekara 23, duk da ana zaton za su fafata da kungiyoyin Bayern Munich da AC Milan a zawarcin dan wasan. (Guardian)
An yi wa dan wasan tsakiya na Ingila, kuma mai taka leda a Nottingham Forest Jesse Lingard, mai shekara 30, tayin komawa Besiktas idan kwantiraginsa ya kare a kakar nan. (Nottingham Post)