BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Mane da Sane sun bai wa hammata iska bayan wasan Man City

Sadio Mane da Leroy Sane

Fri, 14 Apr 2023 Source: BBC

Sadio Mane da Leroy Sane sun yi fada a dakin hutun 'yan wasa, bayan tashi daga Champions League, kamar yadda wasu jaridu suka wallafa ranar Laraba .

Manchester City ce ta doke Bayern Munich 3-0 a wasan farko zagayen quarter finals a gasar zakarun Turai.

Kamar yadda Bild da Sky da wasu jaridun Jamus suka wallafa, 'yan wasan biyu sun bai wa hammata iska, bayan tashi daga karawar har sai da aka shiga tsakaninsu.

Bild cewa ta yi Mane ya naushi Sane tsohon dan kwallon City a fuska, har lebensa ya dan tsage.

Bayern Munich ba ta ce komai ba kan dalilin da ta kai fitattun 'yan wasan nata su kayi fada bayan tashi daga karawa da City.

Bild ta ce rashin jituwar tsakanin 'yan wasan ya fara a cikin fili a Etihad ranar Talata, inda wani hoto ya fayyace lokacin da suke mayar da kalamai a tsakaninsu.

Rashin nasara da Bayern Munich ta yi 3-0, shine mafi muni a Champions League tun bayan 2007.

Bayern mai Champions League shida na fuskantar barazanar ficewa daga gasar bana, bayan da za ta karbi bakuncin wasa na biyu ranar 19 ga watan Afirilun.

Manchester City ba ta daukar Champions League, duk da cewar Pep Guardiola yana da biyu a Barcelona.

Source: BBC