Ma'aikatan jinya da ƙasashe masu ƙarfin arziƙi ke ɗauka daga ƙasashe matalauta "ya wuce gona da iri", a cewar shugaban ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ma'aikatan jinya na duniya.
Kalaman na zuwa ne daidai lokacin da BBC ta gano shaidu kan yadda tsarin kula da lafiyar Ghana ya shiga mawuyacin hali saboda ƙaura da ma'aikatan jinya ke yi daga asibitocin ƙasar.
Ƙwararrun ma'aikatan jinya da yawa sun sulale sun bar ƙasar da ke yankin Afrika ta Yamma don samun ingantattun ayyuka mafi tsoka a ƙasashen waje.
A cikin 2022, ma'aikatan jinya 'yan Ghana fiye da 1,200 ne suka shiga Birtaniya.
Wannan na zuwa ne yayin da Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHS) ke ƙara dogara kan ma'aikatan lafiya daga ƙasashen da ba na Tarayyar Turai ba, don cike guraben aiki.
Ko da yake, Birtaniya ta ce ba a yarda da ɗaukar ma'aikata gadan-gadan daga Ghana ba, amma ta hanyar kafofin sada zumunta ma'aikatan jinya na iya ganin guraben aikin da ake tallatawa a NHS.
Sannan za su iya neman ayyukan kai tsaye. Mawuyacin hali da tattalin arziƙin Ghana ya shiga na iya zama babban sanadi.
Howard Catton daga Majalisar Ma'aikatan Jinya ta Duniya (ICN) ya bayyana damuwa game da yawan ma'aikatan lafiyan da ke barin ƙasashe kamar Ghana.
"A tunani wannan lamari ya wuce gona da iri," kamar yadda ya shaida wa BBC.
"Manyan ƙasashe masu arziƙi kimanin shida ko bakwai na ɗaukar ɗumbin ma'aikatan lafiya daga ƙasashe waɗanda wasunsu su ne mafi rauni kuma ba za su so rasa ma'aikatan jinyansu ba."
Shugabar ma’aikatan jinya a asibitin Lardin Greater Accra, Gifty Aryee, ta faɗa wa BBC cewa sashen kula da masu matsananciyar jinya kaɗai ya rasa ma’aikatan jinya 20 da suka gudu zuwa Birtaniya da Amurka a cikin watanni shida da suka wuce - lamarin da ke tattare da manyan illoli.
"Hakan na shafar irin kulawar da muke bayarwa don har ma mun daina karɓar ƙarin marasa lafiya ba. Kuma ana ɓata lokaci sosai, hakan na kuma haddasa ƙarin mace-mace - marasa lafiya suna mutuwa," in ji ta.
Ta ƙara da cewa sau da yawa, marasa lafiyan da jikinsu ya yi tsanani suna shafe tsawon lokaci a ɗakin kula da masu buƙatar kulawar gaggawa saboda ƙarancin maiaikatan jinya.
Wata ma’aikaciyar jinya a asibitin ta ƙiyasta cewa rabin waɗanda ta kammala karatu da su, sun fice sun bar ƙasar – kuma tana son ita ma ta bi su.
'Duk ma'aikatan jinyarmu masu ƙwarewa sun tafi'
BBC ta gano irin wannan lamari a asibitin Cape Coast.
Mataimakiyar shugabar ma’aikatan jinya a asibitin, Caroline Agbodza, ta ce ta ga ma’aikatan jinya 22 da suka tafi Birtaniya a shekarar da ta wuce.
"Duk ma'aikatan jinyarmu masu ba da muhimmiyar kulawa da sauran ƙwararrun ma'aikatanmu sun tafi. Don haka ba mu da komai - babu ƙwararrun ma'aikatan da za mu yi aiki da su.
Ko gwamnati ta ɗauki sabbin ma'aikata, dole ne sai mun yi fama wajen sake horar da su."
Ƙananan asibitocin ma, gudun hijirar ma’aikatan ya shafe su, saboda ko ma’aikaciyar jinya ɗaya ce ta bar aiki, ba ƙaramar matsala za a samu ba.