BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Masu juyin mulki a Nijar sun kama wasu jami'an hamɓararriyar gwamnati

Flag Of Niger Tutar Nijar

Mon, 31 Jul 2023 Source: BBC

Jam'iyyar PNDS-Tarayya da sojoji suka hamɓarar daga kan mulki ta yi zargin dakarun tsaro sun kama wasu ƙusoshinta inda suke ci gaba da tsare su.

Wata sanarwa da jama'iyyar ta fitar mai ɗauke da sa hannu Mallam Kalla Hanƙurau, babban magatakardan jam'iyyar PNDS, ta zayyana sunayen wasu 'ya'yan Tarayyar da ta ce sojojin sun kama.

A cikinsu har da Alhaji Foumakoye Gado da Mahamane Sani Mahamadou wato Abba. ministan man fetur da Madame Oussieni Hadizatou wato Madam Og, wadda ita ce ministar ma’aikatar tama da ƙarafe da tama.

Lamarin na zuwa ne bayan kama Hama Adamou Souley, ministan cikin gida da Oumarou Mallam Alma, ministan sufuri da kuma wani ɗan majalisar dokoki kuma tsohon ministan tsaro Kalla Mountari.

Sojojin masu juyin mulkin dai suna ci gaba da dakatar da muƙarraban gwamnatin hamɓararren shugaban Nijar Bazoum Mohamed.

A ɓangare guda kuma, bayanai na ci gaba da fitowa game da iƙirarin da sojojin da suka yi juyin mulki cewa, wasu jami'an hamɓararriyar gwamnati da dakarun Faransa, na shirin kai musu hari don kuɓutar da Shugaba Mohamed Bazoum daga fadar gwamnati.

Sojojin na zargin ministan harkokin waje kuma firaministan wucin gadi, Hassoumi Massaoudou da Manjo Midou Gere, kwamandan rundunar sojojin Garde-Sarki na Nijar da kuma wasu jami'an Faransa da hannu a wannan lamari.

A cikin sanarwa mai lamba 14 da kakakin Majalisar mulkin sojin ya fitar sojojin sun yi zargin cewa a cikin tsarinta na neman dalili domin kai hari da ƙarfin soji a Nijar, Faransa da hadin bakin wasu 'yan ƙasar Nijar, sun yi wata ganawa a shalkwatar sojoji na Garde-Sarki, domin su samu izinin da ya dace daga ‘yan siyasa da kuma sojoji.

Sun ce ta haka ne Malam Hassoumi Masaoudou, ya sa hannu a matsayinsa na ministan harkokin waje kuma firaminista wucin gadi kan takardar bai wa dakarun Faransa damar kai hari, domin kuɓutar da shugaban Nijar Mohamed Bazoum da ke tsare.

Haka ma Manjo Kanal Midou Gire kwamandan sojojin na Garde-Sarki shi ma ya sa hannu a madadi hafsan hafsoshin ƙasar, a cewar masu juyin mulkin domin bai wa Faransa izinin kai harin kan fadar shugaban ƙasa.

Source: BBC