BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Masu sa ido kan zaɓen Saliyo sun nuna damuwa bayan wani artabu

Hoton alama

Fri, 23 Jun 2023 Source: BBC

Masu sa ido kan zaɓe a ƙasar Saliyo sun bayyana damuwa game da aukuwar tashin hankali da razanarwa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na ranar Asabar.

Masu sa ido daga Tarayyar Afirka da kuma Ƙungiyar Raya ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas sun fitar wata sanarwa inda suka buƙaci jam'iyyun siyasa da magoya bayansu su tabbatar da aiki da doka.

Sun kuma yi kira ga dakarun tsaro su kasance 'yan ba-ruwanmu a harkar siyasa.

Shugaban ƙasar Maada Bio yana neman takarar wa'adi na biyu, wanda shi ne zaɓen shugaban ƙasa na biyar tun bayan kawo ƙarshen yaƙin basasar Saliyo a shekara ta 2002.

A ranar Laraba, magoya bayan jam'iyyar adawa ta APC sun kara da jami'an tsaro suka yi arangama a kusa da shalkwatar jam'iyyar da ke Freetown.

Jam'iyyar APC ta yi kiran zanga-zangar ne kan abin da ta kira rashin daidaito a cikin tsare-tsaren zaɓe.

Saliyo ta ga jerin tashe-tashen hankula a 'yan watannin nan. A bara, an samu mummunar zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a kan tsadar rayuwa da matsin tattalin arziƙi.

Mutane sun shiga rige-rigen zuwa kasuwanni musamman a babban birnin ƙasar, don sayen kayan abinci kafin zaɓukan na ranar Asabar, kamar yadda mazauna birnin Freetown suka shaida wa BBC.

Lamarin ya zo bayan artabun jami'an tsaro da magoya bayan babbar jam'iyyar adawa, inda aka ba da rahoton cewa aƙalla mutum daya ya mutu.

An rufe wuraren kasuwanci na ɗan wani lokaci ana tsaka da hargitsi kuma yanzu akwai fargabar cewa ana iya samun ƙarin tashe-tashen hankula bayan zaɓen na ranar Asabar.

Sidi Yahya Tunis, mai magana da yawun jam'iyyar adawa ta All People's Congress (APC), ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa 'yan sanda sun kashe wani magoyin bayan jam'iyyar.

Wani bidiyo ba da a tantance shi ba na yamutsin ya nuna wani mutum magashiyan wanda aka ga tamkar an harbe shi a wuya.

Daraktan 'yan sanda sashen aikace-aikace Mohamed Braima Jah ya ce 'yan sanda ba su yi harbi ba, ya ma zargi masu zanga-zanga da yin harbi: "Biyu daga wata bindigar fistol da kuma uku daga wata bindiga ƙirar AK-47."

Kafofin yaɗa labarai a cikin gida sun ce an kama mutane kimanin 66.

Ita dai jam'iyyar APC ta yi zargin cewa kundin bayanan hukumar zaɓen Saliyo ba daidai yake ba. Mutane kimanin miliyan 3.4 ne aka yi musu rijista don kaɗa ƙuri'a.

Source: BBC